Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in Falasdinawa ya yi Allah wadai da sabon yunkurin Netanyahu na mamaye yammacin kogin Jordan
2019-08-27 11:02:23        cri
A jiya Litinin babban jami'in Falastinawa ya yi Allah wadai da kudurin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na sabon shirin mamaye matsugunan Falastinawa a yammacin kogin Jordan.

Tun da farko a wannan rana, Netanyahu ya baiwa ofishinsa umarnin shirin gina sabbin matsugunan Yahudawa kimanin 300 a yankin Dolev, kusa da birnin Ramallah na al'ummar Falasdinawa wanda Yahudawa suka mamaye a yammacin kogin Jordan.

Netanyahu ya ce, an dauki wannan mataki ne domin ramuwar gayya kan mummunan harin bam da Falastinawa suka kaddamar a ranar Juma'a, wanda ya yi sanadiyyar hallaka wata yarinya bayahudiya 'yar shekaru 17 da haihuwa, kana da raunata dan uwanta da mahaifin yarinyar.

Domin mayar da martani, Hanan Ashrawi, mamban kwamitin gudanarwar kungiyar fafutukar ceto al'ummar Falastinawa, ya bayyana matakin da mista Netanyahu ya dauka a lokacin taron manema labarai da cewa, wauta ne da neman tada rikici ta hanyar nuna cin zali. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China