Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yanayin muhallin ruwan kasar Sin yana kara kyautatuwa
2019-08-26 11:56:16        cri

Wani rahoton mahukuntan kasar Sin ya bayyana cewa, yanayin ingancin albarkatun ruwa a manyan tekuna, da tafkuna, da koguna, da mashigar ruwan kasar Sin yana kara kyautatuwa sannu a hankali, sai dai yanayin kula da muhallin ruwan yana cike da rashin tabbas.

Rahoton wanda tawagar masu bincike da bibiyar yadda ake yin aikin aiwatar da bada kariya daga gurbacewar ruwa, karkashin jagorancin babban kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin NPC, kana babban kwamitin 'yan majalisun dokokin kasar Sin ya fitar.

Daga watan Afrilu zuwa watan Yuni, hukumar dake sanya ido wajen tsara dokokin ta kasu gida hudu, inda ta ziyarci wasu larduna 8, da suka hada da Sichuan, Jiangsu, Hunan, Hebei, Guangdong, Anhui, Yunnan and Guizhou, domin aiwatar da tsara dokokin kula da muhallin albarkatun ruwa.

A cewar rahoton, a shekarar 2018, kashi 71 bisa 100 na yanayin albarkatun ruwan kasar yana da matukar kyau, kana ingancin ruwa a manyan tekuna, da tafkuna, da mashigar ruwan kasar yana da kyau matuka. To sai dai kuma, rahoton ya lura cewa karancin aiwatar da dokoki sun kasance babban kalubale, kuma baki daya yanayin muhallin albarkatun ruwan kasar Sin yana cikin yanayin rashin tabbas. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China