Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai dace a umarci kamfanonin Amurka su janye jiki daga kasar Sin ba
2019-08-25 19:57:26        cri

Kwanan baya Amurka ta sanar cewa, za ta kara sanya harajin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin kasar Sin da za ta shigo da su kasar wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 300, domin kare moriyarta, kasar Sin ta dauki matakin mayar da martani, a don haka, wasu Amurkawa sun ba da umarni ga kamfanonin kasarsu da su janye jiki daga kasar Sin, wannan mataki ne da gwamnatin kasar Amurka ta dauka wanda ke cike da makarkashiyar siyasa, shi ya sa ba ma kawai matakin ya kawo cikas ga gudanarwar harkokin kamfanonin kasar Amurka ba, har ma ya lalata tsarin tattalin arzikin duniya, ana iya cewa, umarnin ya sabawa tsarin tattalin arzikin kasuwa, har masanan tattalin arzikin Amurka sun yi adawa da shi.

Yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba mai inganci, haka kuma yana taka babbar rawa a cikin tsarin sana'o'in kasa da kasa, a don haka kasuwar kasar Sin ta fi jawo hankalin masu zuba jarin kasashen duniya baki daya.

Hakika dalilin da ya sa tattalin arzikin Amurka bai samu ci gaba yadda ya kamata ba shi ne domin ba ta tsara tsarin tattalin arzikin da ya dace da yanayin da kasar ke ciki ba, matakan da wasu Amurkawa suka dauka kamar na kara sanya haraji, da matsa lamba ga sauran kasashe ba za su iya dakile kalubalen da Amurka take fuskantar ba, haka kuma ba za su iya tilastawa kamfanonin Amurka dake kasar Sin su janye jiki daga kasar ta Sin ba, wata kila za su sa kamfanonin kasar Amurka su janye jiki daga kasar Amurka, ko shakka babu Amurkawan ba su so ganin aukuwar lamarin ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China