Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An zabi Ho Iat Seng a matsayin gwamnan Macao na 5
2019-08-25 16:50:46        cri

Yau 25 ga wata, an gudanar da zaben gwamnan yankin musamman na kasar Sin Macao na biyar a cibiyar taron kasa da kasa ta cibiyar wasannin motsa jiki ta gabashin Asiya, inda aka zabi Ho Iat Seng a matsayin gwamnan yankin na biyar bisa kuri'u masu rinjaye kimanin 392 da ya samu.

Bisa dokar zabar gwamnan yankin Macao, dole ne adadin mambobin hukumar zabe wadanda suka jefa kuri'u ya kai kashi 2 bisa 3, kana dole mai tsayawa takarar ya samu kuri'u sama da 200, wato rabin adadin mambobin hukumar, yau ma daukacin mambobin 400 sun jefa kuri'unsu.

An kaddamar da zaben da misalin karfe 10 na safiyar yau, an shafe mintoci talatin ana jefa kuri'un, daga bisani, bayan kididdigar da aka yi, hukumar zaben ta sanar cewa, Ho Iat Seng ya samu kuri'un 392, wadanda suka kai kaso 98 bisa dari, ya yi nasarar lashe zaben inda ya kasance sabon gwamnan yankin na Macao.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China