Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta fara aiwatar da tsarin "babban mai lura da gandun daji"
2019-08-23 16:36:12        cri
Shugaban hukumar dake kula da gadun daji da yankuna masu tsirrai ta kasar Sin, ya bayyana aniyar kasar na fara aiwatar da tsarin kare gandun daji ta amfani da babban jami'in gandun daji. Bisa tsarin, nan da shekarar 2020, kasar za ta cimma nasarar kare dazukan ta na ainihi, da kafa muhimman tsare-tsare, na farfado da albarkatun daji.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a birnin Beijing, yana mai cewa tsarin kafa "babban jami'in gandun daji", na kunshe da daukar matakai na shugabanci a matsayi na zartaswa don kare dazuka, da kula da su, da gudanar da bincike a kan dazukan na tsawon lokaci, tare da tanadar hukunci ga ayyukan da suka jibanci barnata dazukan.

Sin na da fadin dajin ainihi da ya kai sama da hekta miliyan 190, adadin da ya kai kaso 64 bisa dari na fadin dazukan dake kasar. A daya hannu kuma, Sin ta samu ci gaba mai armashi a fannin kare nau'ikan gandun daji na ainihi. Hakan kuwa ya biyo bayan yawan bishiyoyin da ake kara shukawa a kasar, wanda ya kai matsayin farko a duniya.

Ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan fadin dazukan dake Sin ya kai kaso sama da 20 bisa dari na kasar. An kuma fadada kariyar ingancin ruwa da kasa, yayin da kuma muhallin rayuwar halittu daban daban dake kasar ke kara kyautata, ana kuma kara shuka tsirrai masu samar da kyakkyawan sakamako.

Jami'in ya ce kasar Sin ta cimma burin nan na samar da yanayin "Ruwa mai tsafta da tsaunuka masu ni'ima" bisa rungumar da al'ummar kasar suka yiwa tsarin. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China