![]() |
|
2019-08-23 11:28:10 cri |
'Yan wasan za su shiga wasanni 56, a fannoni 6 da suka hada da: sufuri da tsare-tsare, da zanen taswirar gini, da aikin kere-kere da injiniya, da samar da bayanai da sadarwa, da fasahohin hannu da kwalliya da kuma hidimomin al'umma da na daidaikun mutane.
Wannan ne karo na 5 da kasar Sin ta halarci gasar nuna basira ta duniya.
Jimilar 'yan wasa 1,355 daga kasashe da yankuna 69 ne za su halarci gasar ta kasa da kasa, da taimakon alkalan wasa 1,304 da masu tafinta 394 daga kasashen da ba sa amfani da Turancin Ingilishi. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China