Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar Lingang ta yankin gwajin ciniki maras shingen Shanghai za ta inganta karfin ci gaban tattalin azikin duniya
2019-08-22 10:37:24        cri

An kaddamar da cibiyar aikin Lingang, ta yankin gwajin cinikayya maras shinge na birnin Shanghai na kasar Sin a ranar 20 ga wata, inda za a kafa cibiyar tattalin arziki ta musamman wadda za ta yi tasiri ga kasuwar kasa da kasa, haka kuma za ta sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci, tare kuma da inganta karfin ci gaban tattalin arzikin duniya.

Cibiyar Lingang ta yankin gwajin ciniki maras shinge tana kudu maso gabashin birnin Shanghai na kasar Sin, wadda take da nisan kilomita 75 daga cibiyar birnin, an kafa ta ne a wurin dake hada mashigar teku ta kogin Yangtse da gabar tekun Hangzhou, yayin da tashar saukar jiragen saman kasa da kasa ta Pudong tana arewancin cibiyar, kana a kudancinta kuma tashar ruwan teku mai zurfi ta Yangshan ce. Ana iya cewa, cibiyar Lingang ta nuna fiffiko matuka a bangaren sufuri, haka kuma an raba cibiyar gidaje da dama; kamar su babbar unguwa, da unguwar kere-kere ta hanyar yin amfani da fasahar kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam, da unguwar raya tattalin arziki bisa shirin da aka tsara, da unguwar kiyaye muhalli ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, da unguwar kirkire-kirkiren kimiyyar teku da sauransu.

Mataimakiyar babban sakataren gwamnatin birnin Shanghai, kuma zaunannen mataimakin darektan cibiyar Lingang Zhu Zhisong ya yi mana bayani da cewa, sabuwar cibiyar Lingang za ta nuna kwazo da himma domin raya birnin Shanghai, da wasu biranen lardunan Jiangsu da Zhejiang da Anhui, wadanda ke kusa da gabar kogin Yangtse, yana mai cewa, "Sabuwar cibiyar Lingang ta yankin gwajin cinikayya maras shinge na birnin Shanghai, za ta mai da hankali kan ci gaban tattalin arziki mai inganci a birnin Shanghai, da wasu biranen lardunan Jiangsu da Zhejiang da Anhui, wadanda ke kusa da gabar kogin Yangtse. Haka kuma za ta taka rawa a bangarori uku; wato tabbatar da sabon ci gaban birnin Shanghai bisa manyan tsare-tsare, da inganta sabon karfin ci gaban birnin, da kuma tsara sabon tsarin ci gaban birnin na Shanghai. Kana za ta ba da gudumowa ga cudanyar tattalin arzikin yankunan dake gabar tekun gabashin kasar Sin, har ma za ta kasance garin dake sahun gaba a yankin Asiya da tekun Pasifik."

A watan Mayun shekarar 2018, an yi rajistar kamfanin Tesla reshensa a birnin Shanghai a cibiyar Lingang, daga baya an fara gina kamfanin cikin watanni shida. Mataimakin shugaban kamfanin samar da motoci masu amfani da wutar lantarki na Tesla Tao Lin tana ganin cewa, manufofi masu inganci da ake aiwatarwar a cibiyar Lingang, sun samar wa kamfanonin kasa da kasa damar samun ci gaba, haka kuma sassan biyu wato cibiyar Lingang da kamfanonin za su samu moriya tare, tana mai cewa, "Yankin gwajin cinikayya maras shinge ya kan nuna fiffiko a fannin kirkire-kirkire, ana iya yin gwaji a nan, a don haka mun samu damammaki da dama wajen yin amfani da sabbin fasahohin zamani a nan. Idan mun gano cewa, sabbin fasahohi, ko sabon tsarin kasuwanci ya dace da muhallin kasar Sin, to za su amfani ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Yanzu an kafa kamfanin Tesla a kasar Sin, ko shakka babu zai kawo damar ci gaba ga cibiyar Lingang, kuma sassan biyu za su samu moriya tare."

Abu mai faranta rai shi ne, tun bayan da aka kafa yankin gwajin cinikayya maras shinge a birnin Shanghai kafin shekaru shida da suka gabata, an kammala ayyukan gyaran fuska da yawansu ya kai 306, bisa tushen kirkire-kirkiren tsarin hukumomin gwamnatin kasar.

Bisa shirin da aka tsara, adadin kudin da za a samu a cibiyar nan da shekarar 2035, zai kai kudin Sin yuan biliyan 1000. Ministan kasuwancin kasar Sin Zhong Shan ya bayyana cewa,"Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin za ta yi kokari tare da gwamnatin birnin Shanghai, da sauran hukumomin da abun ya shafa, wajen ingiza gyaran fuska, da kara karfafa kirkire-kirekiren tsarin gudanar da harkokin kamfanoni, ta yadda za a magance hadarorin da za su faru, tare kuma da cimma burin da aka tsara a shekarar 2025 da shekarar 2035, wato gina sabuwar cibiyar Lingang, har ta kai ga kasancewa cibiyar tattalin arziki ta musamman, wadda za ta yi tasiri sosai ga kasuwar kasa da kasa."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China