Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Bai dace a fake da guzuma ana harbin karsana ba
2019-08-21 20:02:59        cri

Tun lokacin da Amurka ta tayar da takaddamar cinikayya tsakaninta da kasar Sin, wasu 'yan siyasa da masu fada a ji a kasar, suke fito da wasu hanyoyi na ganin bayan wasu kamfanonin kasar Sin da ma kokarin shafawa mahukuntan kasar ta Sin kashin kaji da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da sauransu.

Batu na baya-bayan nan shi ne, kokarin shiga harkokin cikin gidan kasashen Uganda da Zambiya ta hanyoyin da ba su dace ba, matakan da ka iya shafar alakar kasashen na Afirka da kamfanonin kasar Sin.

Sanin kowa ne cewa, kowa ce kasa mai cikakken 'yanci tana da ikon tafiyar da harkokin tsaronta da na al'ummominta bisa doka, kamar yadda kasashen dake kiran kansu manyan kasashe a duniya irinsu Amurka ke yi, wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama'arsu, ta hanyar Makala na'urorin sanya ido ko CCTV a kan tituna ko muhimman wurare.

Don haka, kokarin da wasu kasashen yammacin duniya ke yi na neman tsokana da shafawa kasar Sin da kasashen Afrika kashin kaji, ba zai yi tasiri ba.

Labarin da jaridar "The Wall Street Journal" ta kasar Amurka ta wallafa wai, kamfanin Huawei na kasar Sin na amfani da fasaha da kayayyakinsa, don taimakawa gwamnatocin wasu kasashen Afrika kamar Uganda da Zambiya wajen sa ido kan abokan gabansu dake cikin kasashen, wani salo ne na neman takalar fada.

Kamfanin Huawei dai ya ba da amsa, kuma gwamnatocin wadannan kasashe wato, Uganda da Zambiya, su ma sun bayyana cewa, labarin da aka wallafa ba shi da hujja ko wani dalili, kuma karya ne tsagwaronta.

Idan har Amurka ta amince da amfani da irin wadannan fasaha da kayayyaki a cikin gidanta, me ya sa sauran kasashe ba za su yi hakan ba? Kuma har wasu ke zargin cewa hakan wani mataki ne na sa ido?

A matsayinta na kafar yada labarai da ta shahara a duniya, labarin da Jaridar "The Wall Street Journal" ta wallafa ya zubar mata da mutunci kwarai da gaske.

Hausawa na cewa, mai daki shi ya san inda ke masa yoyo, kasashen Afrika sun fi kowa sanin bukatunsu, kuma suna mai da hankali sosai kan muradu da harkokinsu na tsaro, don haka babu ruwan wasu kasashe da harkokin cikin gidansu. Kowa ya kashe wutar gabansa.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China