Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da taron na'urar mutum mutumi na duniya a Beijing
2019-08-21 10:51:19        cri

A jiya Talata ne aka kaddamar da babban taron na'urar mutum mutumi, wato na'urori masu sarrafa kan su da kan su na kasa da kasa, na shekarar 2019 a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, inda ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin Miao Wei ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana sa kaimi ga cudanya, da hadin gwiwar dake tsakanin kamfanoni da hukumominta da na sauran kasashen duniya, domin ciyar da sana'ar samar da na'urar mutum mutumi gaba yadda ya kamata.

Ana gudanar da babban taron na'urar mutum mutumi wato na'urori masu sarrafa kan su na kasa da kasa na shekarar 2019 a nan birnin Beijing tsakanin ranar 20 zuwa 25 ga wata. Babban taken taron shi ne "raya fasahar kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam mai inganci a sabon zamani mai bude kofa", inda za a shirya dandalin tattaunawa daban daban, a sa'i daya kuma, za a shirya bikin baje kolin na'urorin mutum mutumi na kasa da kasa, da babbar gasar samar da na'urorin mutum mutumi.

A wurin bikin kaddamar da babban taron da aka gudanar jiya, shugaban asusun nazarin na'urar mutum mutumi na kasa da kasa Oussama Khatib ya bayyana cewa, a cikin shekarun bayan bayan nan, kasashen duniya suna sanya kokari matuka, inda suka dauki matakai a jere domin inganta fasahar samar da na'urar mutum mutumi, tare kuma da raya sana'ar samar da na'urar mutum mutumi, a don haka kasuwar na'urar tana samun ci gaba sannu a hankali.

Fasahar samar da na'urar ita ma tana samun kyautatuwa cikin sauri, har ta kai ga yin babban tasiri ga rayuwar bil Adama. Oussama yana mai cewa, "A shekarar 2018, adadin kudin da aka samu daga kasuwar sayar da na'urar mutum mutumi a fadin duniya sun kai dala biliyan 30. Kasar Sin ta kasance kasuwar na'urar mutum mutumi mafi amfani ga masana'antu mafi girma a duniya, haka kuma kirkire kirkiren fasahar samar da na'urorin a kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri, yayin da kasar ke samar da gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya a wannan fanni. Ana iya cewa, kasar Sin tana taka babbar rawa a bangaren kirkire-kirkiren kimiyya da sana'ar samar da na'urorin mutum mutumi."

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a cikin watanni shida na farkon shekarar bana wato shekarar 2019, adadin kudin da aka samu daga kasuwar sayar da na'urar mutum mutumi a fadin duniya sun kai dala biliyan 14 da miliyan 400. Adadin da aka samu a kasuwar kasar Sin kuwa ya kai dala biliyan 4 da miliyan 250.

Sakataren 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, a kungiyar masu aikin kimiyya da fasaha ta kasar Huai Jinpeng ya yi mana bayani cewa, a halin da ake ciki yanzu, sana'ar samar da na'urar mutum mutumi tana samun ci gaba cikin sauri, saboda ana amfani da sabbin fasahohi, haka kuma ana samar da wasu sabbin na'urorin, a cewarsa: "Tsarin samar da na'urorin mutum mutumi yana kara kyautatuwa, har ta kai ana amfanin sabbin na'urorin daga duk fannoni a fadin duniya. Kana an fi mai da hankali kan wasu sabbin bangarori, yayin da ake kokarin yin kirkire-kirkire. Daga sakamakon da aka samu yanzu, an lura cewa, aikin nazari da raya fasahar samar da na'urar mutum mutumi ya kyautata a bayyane, kuma kwararru da abin ya shafa su ma sun karu cikin sauri."

A shekarar 2018, adadin na'urorin mutum mutumi masu amfani ga masana'antun da aka samar a kasar Sin ya kai dubu 148, adadin da ya kai kaso 38 bisa dari, cikin daukacin na'urori makamantansu a fadin duniya. A cikin jawbin da ya gabatar yayin bikin kaddamar da taron, ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin Miao Wei ya bayyana cewa, duk da cewa, sana'ar samar da na'urar mutum mutumi ta kasar Sin tana bukatar ingantuwa, amma sana'ar za ta ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri, haka kuma gwamnatin kasar Sin tana sa kaimi kan cudanya, da hadin gwiwar dake tsakanin kamfanoni da hukumominta da na sauran kasashen duniya, domin ciyar da sana'ar gaba yadda ya kamata, yana mai cewa, "Yanzu kasar Sin tana ingiza ci gaban sana'ar kere-kere, a don haka ya dace a kara raya sana'ar kere-kere, ta hanyar yin amfani da fasahar kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam. Muna fatan kamfanoni da hukumomi na kasar Sin da na kasashen ketare, za su kara gudanar da cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninsu, domin ciyar da sana'ar samar da na'urar mutum mutumi gaba a fadin duniya yadda ya kamata."

An fara kiran babban taron ne tun daga shekarar 2015, inda kwararru da 'yan kasuwa sama da 1000, da suka zo daga kasashe da hukumoni daban daban na kasa da kasa, suka yi tattaunawa mai zurfi kan aikin, da ma yadda za a ciyar da sana'ar gaba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China