Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Koyon Sinanci daga "Xinwen Lianbo"
2019-08-19 11:33:51        cri

Shirin labaran talabijin na rana-rana da ake watsawa a nan kasar Sin mai suna "Xinwen Lianbo", ya sha sharhi daga kafafen zumunta na kasar, bayan da ya gabatar da wasu jerin gajerun bayanai ta shirye-shiryensa na rana-rana–sai dai kuma shirin ya haifarwa masu fassasa tarin kalubale.

Tsarin gabatar da bayanan shirin ya ja hankalin matasa masu kallo, wadanda ke bin sa sau da kafa a kafafen yanar gizo, tamkar masu kallon irin shirye-shiryen nan masu dogon zango da kafafen nuna fina-finai ke haskawa.

Wannan shiri har ya kai ga jan hankalin kafafen watsa labarai na kasa da kasa. Rahotanni sun tabbatar da cewa, kafafen "The Wall Street Journal", da "The New York Times", da BBC, da CNN, da "Fox" da ma wasu kafafen na daban, sun rika gabatar da bayanai da suka yanko daga shirin na "Xinwen Lianbo". To sai dai kuma, wasu sassan shirin na gamuwa da matsalar fassara daga masu magana da harshen Ingilishi. An ce masu fassara kan gamu da sarkakiyya yayin da suke kokarin fayyace ma'anar wasu jumloli da Ingilishi idan an bayyana su da harshen Sinanci.

Domin taimakawa masu son fahimtar harshen al'adun Sinanci, mun fassara wasu daga jumloli daga salon labaran "Xinwen Lianbo".

喷饭

Pen fan (Wani abu da zai iya sanyawa ka tofar da shinkafar ka) na nufin "Abun dariya" ko "shidewa da dariya."

满嘴跑火车

Man zui pao huo che (Bakin ka cike yake da jirgin kasa) na nufin "Kana furta kalaman shirme."

扎轮胎

Zha lun tai (yanka taya) –Daukar fansa.

遮羞布

Zhe xiu bu (tufafin kafadu) – Gaban wando.

裸奔

Luo ben (layuka masu launi) – Bayyana ainihin halin ka.

满地找牙

Man di zhao ya – yi wa mutum dukan kawo wuka.

合则两利,斗则俱伤

He ze liang li, dou ze ju shang – cimma riba daga hadin gwiwa, da yin hasara daga takaddama.

躲得过初一,躲不了十五

Duo de guo chu yi, duo bu liao shi wu – Kana iya guduwa amma ba za ka taba buya ba.

天若欲其亡,必先令其狂

Tian ruo yu qi wang, bi xian ling qi kuang – Wadanda aka nufa da lalacewa sai sun fara yin hauka tukuna.

脚底抹油

Jiao di mo you – Sulalewa.

青山遮不住,毕竟东流去

Qing shan zhe bu zhu, bi jing dong liu qu – Har kullum yanayi na bin tsarin sa na ainihi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China