Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayani game da kare hakkin masu bukata ta musamman a kasar Sin
2019-08-22 17:07:38        cri

A kwanakin baya ne, ofishin watsa labarai na majalisar zartaswar kasar Sin, ya fitar da takardar bayanai, game da kokarin da kasar ke yi cikin shekaru 70, dangane da kare hakkokin masu bukata ta musamman.

Jigon takardar bayanin, shi ne "Daidaito, tafiya tare, da kuma raba daidai: shekaru 70 na kare hakkokin masu bukata ta musamman a jamhuriyar al'ummar kasar Sin."

Yanzu haka dai Sin na da al'umma masu bukata ta musamman da yawan su ya kai miliyan 85. Kuma takardar bayanin ta nuna cewa, cikin shekaru sama da 70 tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, jami'iyyar JKS da gwamnatin Sin, na sanya bukatun al'ummar kasar sama da komai, ta hanyar ba da kulawa ga rukunin al'ummu masu fama da wahalhalu, tare da shigar da su, da damawa da su, da samar musu damar cin gajiya daga sassan ci gaban tattalin arzikin kasar.

Takardar ta kuma ce, za a ci gaba da aiwatar da matakan inganta tsare tsare na kare bukatun wadannan rukuni na al'umma, ba tare da nuna wariya ba, da tabbatar da kyautatuwar rayuwar su, da inganta yanayin da suke ciki, tare da tabbatar da cewa, sun samu zarafin shiga a dama da su a harkokin da suka shafi ci gaban kasa, da raba moriyar hakan daidai wa daida da sauran muhimman fannoni na ilimi, a lafiya da sauransu. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China