Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Ci gaban Fasahohi Na Tura Tattalin Arzikin Kasar Sin Gaba
2019-08-15 16:34:23        cri

Wasu alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta gabatar dangane da yanayin tattalin arzikin kasar sun nuna cewa, cikin watanni 7 na farko na bana, karuwar masana'antun kasar masu alaka da fasahohin zamani ta kai kashi 8.7%, wadda ta fi karuwar sauran fannonin masana'antu da kashi 2.9%. Sa'an nan jarin da ake zuba wa sana'ar samar da kayayyakin fasahohin zamani, da bangaren samar da hidima na fasahohi da suka ci gaba, sun karu da kashi 11.1% da kashi 11.9%, inda karuwarsu ta wuce matsakaicin karuwar zuba jari da kashi 5.4% da kuma kashi 6.2%. Har ila yau, karuwar kudin shiga da aka samu a bangarorin samar da hidimomi na fasahohin zamani, da aikin hidima mai alaka da wasu manyan tsare-tsaren kasa, dukkansu sun wuce kashi 10%. Wadannan misalai sun shaida cewa, tabarbarewar yanayin tattalin arzikin duniya ba ta hana kasar Sin samun ci gaba ba, ganin yadda wasu sabbin sana'o'i masu alaka da fasahohin zamani ke kara taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki mai inganci a kasar Sin, da baiwa kasar damar tinkarar kalubaloli daban daban.

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana kokarin canza salonta daga "kasa mai masana'antu" zuwa "kasar dake da masana'antu masu inganci", don dacewa da sauye-sauyen fasahohi a duniya.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, daga shekarar 2015 zuwa 2017, matsakaicin adadin karuwar ci gaban sana'o'i masu alaka da fasahohin zamani a kasar Sin ya karu da kaso 28 cikin dari. A shekarar bara, yawan kudaden da aka samu daga sabbin masana'antu, sabbin sana'o'i, da sabbin kasuwanci ya kai kaso 16.1 cikin dari na jimilar GDPn kasar Sin, wanda ya karu da kaso 0.3 bisa na shekarar 2017. Kana, gudummawar da sabbin masana'antu, sabbin sana'o'i, da sabbin kasuwanci suka bayar wajen samar da guraben aikin yi ta wuce kashi 2 cikin kashi 3. Har ila yau, a cikin jerin sunayen kasashen duniya da suka yi fice ta fuskar yin kirkire-kirkire a shekarar 2019, wanda hukumar kula da harkokin 'yancin mallakar fasaha ta kasa da kasa ta fitar, kasar Sin ta ci gaba zuwa matsayi na 14, kuma ta rike wannan matsayi cikin shekaru 5 a jere. Ta kuma zama na farko a duniya a fannonin yawan 'yanci mallaka fasaha, hanyoyin samun riba, tamburan kaya masu zaman kansu da tsara kayayyakin masana'antu, shigi da ficin kayayyakin fasahar zamani da na kirkire-kirkire. Kamfanonin fasahar zamani da kamfanonin da ke da kyakkyawar makoma masu yawa suna samun saurin bunkasuwa. A shekarar bara, kamfanin Huawei ya gabatar da takardar bukatar neman 'yancin mallaka fiye da 5400, wanda ya zama na farko a duniya. Kamfanin ya kuma kera sabuwar manhajar wayar salula da ya kirkiro da kansa mai suna HarmonyOS, lamarin da ya nuna kyakkyawar kwarewar kamfanonin Sin ta fuskar yin kirkire-kirkire da yin takara.

Kasar Sin na kara samun sabon kuzari a 'yan shekarun nan, al'amarin da ya nuna irin nasara da kasar ta samu wajen aiwatar da manufar neman bunkasuwa ta hanyar yin kirkire-kirkire. Kasar Sin na nuna himmatuwa wajen bada kwarin-gwiwar yin kirkire-kirkiren fasahohi, ciki har da kara nuna goyon-baya ga harkokin hada-hadar kudi, da nazarin wasu muhimman fasahohin zamani, da gaggauta amfani da sakamakon kimiyya da fasaha, tare kuma da baiwa kamfanoni kwarin-gwiwar su fadada hadin-gwiwa da kasashe daban-daban a fannin yin kirkire-kirkire. Duk wadannan abubuwa sun samar da wani kyakkyawan muhalli na kara raya tattalin arziki, da inganta tushen tattalin arzikin kasar ta Sin.

Amma abun bakin ciki shi ne, wasu 'yan kasashen yammacin duniya wadanda suka yi biris da hakikanin halin da kasar Sin take ciki yanzu, suna furta kalaman karya kan saurin karuwar tattalin arzikin kasar. Wato, yayin da tattalin arzikin Sin ke samun bunkasuwa cikin saurin gaske, wadannan mutane suna ikirarin cewa wai Sin na kawo barazana ga sauran kasashen duniya. Amma idan tattalin arzikin Sin ya ci gaba yadda ya kamata, wadannan mutane za su ce kasar Sin za ta durkushe. Duk wadannan kalaman, ba kawai na sabawa ka'idojin ci gaban tattalin arziki ba, har ma na shafawa kasar Sin kashin kaji. Hakika, ya kamata wadannan mutane su kara lura da tattalin arzikin kasashensu maimakon na kasar Sin. Abin da Bahaushe ke cewa, "kowa ya kashe wutar bagansa".

Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Amurka ta fitar sun nuna cewa, karuwar tattalin arzikin kasar a rubu'i na biyu na bana ta kai kaso 2.1 bisa dari, kasa da kaso 3.1 bisa dari a rubu'i na farko, lamarin da ya shaida cewa, takaddamar cinikayya ta riga ta kawo illa ga kasar a bangarorin fitar da kayayyaki ketare da zuba jari.

Ranar 14 ga watan, an ba da labari cewa, ribar takardun lamunin Amurka na tsawon shekaru goma da na tsawon shekaru biyu wadanda Amurka ta sayar da su ne don ta biya bashin da ake binta ta ragu, ribar takardun lamunin na tsawon shekaru talatin ita ma ta ragu matuka, wannan shi ne karo na farko da kasar Amurkan ta gamu da wannan matsala tun bayan shekarar 2007, ana iya cewa, kasuwar takardun lamunin kasar tana cikin hadari, har ma an yi hasashen cewa, kila tattalin arzikin Amurka zai shiga mawuyacin hali a cikin watanni 12 masu zuwa.

Sakamakon binciken da jaridar Wall Street ta yi a kwanakin baya bayan nan ya nuna cewa, masanan tattalin arziki sun yi hasashen cewa, iyuwar tabarbarewar tattalin arzikin Amurka za ta karu daga kaso 30.1 bisa dari a watan Yulin bana zuwa kaso 33.6 bisa dari a cikin watanni 12 masu zuwa, adadi mafi girma tun bayan da jaridar ta fara gudanar da binicken a shekarar 2011.

Ba wanda zai ci nasara a takaddamar ciniki, tarihi da kuma halin da ake ciki yauzu sun shaida wadannan kalamai. Ko da yake, tattalin arzikin Sin na fuskantar kalubalen koma baya, amma yana kokarin rike matsayinsa da yin gyaran fuska kamar yadda aka tsara. Sin tana kokarin sauya hanyarta ta samun bunkasuwa mai inganci, hakan ya sa za ta nuna karin kuzari da himma da kwazo a wannan fanni, kuma zai samarwa fadin duniya zarafi mai kyau. A hannu guda kuma, duk wanda ya tada takaddamar ciniki bisa halayyar ra'ayi na kashin kai da ba da kariya ga harkokin cinikayya, shi ne zai dandana kudarsa. (Bello, Tasallah, Murtala, Jamila, Amina)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China