Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bullo da sunayen fitattun kamfanonin Intanet guda dari dake kan gaba a kasar Sin
2019-08-15 14:04:48        cri
Kungiyar kula da harkokin yanar gizo ta Intanet ta kasar Sin da cibiyar kula da tsaron Intanet da raya masana'antu ta ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar, sun fitar da wani rahoto cikin hadin-gwiwa, dangane da ci gaban wasu fitattun kamfanonin Intanet guda dari wadanda ke kan gaba a kasar a shekarar 2019. Rahoton ya yi nuni da cewa, kamfanonin Intanet na kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen sabunta fasahohi da lalibo sabbin hanyoyin neman bunkasuwa, a wani kokari na jagorantar ayyukan yin kirkire-kirkire a duk fadin kasar ta Sin.

Alkaluman sun nuna cewa, yawan kudin da wadannan kamfanonin Intanet guda dari suka samu daga harkokin Intanet ya kai Yuan triliyan 2.75, wanda ya ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki irin na Intanet na kasar Sin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China