Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa Check ya kulla alaka da Facebook
2019-08-15 09:21:12        cri
Kafar tantace sahihan labarai mai zaman kanta ta farko a Afirka mai suna "Afirca Check" ta sanar da kulla alaka da shafin sada zumunta na Facebook, da nufin tantance sahihancin labaran da ake sanyawa a kafofin sada zumunta ta yadda za a rage baza labarai na karya.

Shugaban tsara manufofi na shafin sada zamunta na facebook dake Afirka, Kojo Boakye ne ya sanar da hakan, yana mai cewa, an fara kaddamar da shirin ne a shekarar 2018 a kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar sahara, ciki har da Afirka ta Kudu da Kenya da Najeriya da Senegal da Kamaru, don baiwa masu mu'amala da shafin damar tantace ko bayanan da aka sanya na gaskiya ne ko a'a.

Ya ce, shafin na Facebook zai ci gaba da daukar matakan da suka dace, a kokarin da suke yi na yakar labaran karya da ake ta yadawa a shafin, ta yadda zai samu goyon baya, samar da tsaro da fadakar da daukacin al'umma.

A halin yanzu shirin, ya kunshi harsunan Yarabanci da Igbo a Najeriya, sai harshen Swahili a kasar Kenya, Wolof a Senegal, yayin da aka sanya harsunan Afrikaans, da Zulu da Setswana da Sotho da Northen Sotho da Southern Ndebele da ake magana da su a Afirka ta Kudu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China