Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin kasar Sin dake samun ci gaba ba tare da tangarda ba yana da karfin tinkarar kalubaloli
2019-08-14 19:56:00        cri

A yau Laraba, hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da alkaluma game da yadda tattalin arzikin kasar yake bunkasa cikin farkon watanni 7 na bana. Alkaluman sun bayyana cewa, har yanzu tattalin arzikin kasar na samun bunkasuwa ba tare da tangarda sosai ba kamar yadda ake fata.

A lokacin da kasar Amurka ke kara tsananta rikicin cinikayya tsakaninta da kasar Sin, kuma yanayin duniya yake cikin hali maras tabbas, tattalin arzikin kasar Sin da yake da karfin tinkarar kalubaloli, da kuma na kawar da matsaloli ya bayyana cewa, kasar Sin tana da imani game da bunkasa tattalin arziki kamar yadda ya kamata.

Yanzu, halin da kasashen duniya ke ciki ya kara tsananta, kuma kasar Sin ta kau da matsaloli iri iri domin tabbatar da ganin tattalin arzikinta ya ci gaba da samun bunkasuwa ba tare da tangarda sosai ba. Sabo da har yanzu kasar Amurka tana tsananta rikicin cinikayya tsakaninta da sauran kasashen duniya, kana tattalin arzikin kasashen duniya ya shiga hali maras tabbas. Sakamakon haka, hukumomin kasa da kasa, kamar su IMF da bankin duniya, sun rage saurin karuwar tattalin arzikin kasashen duniya a bana, da kuma a shekara mai zuwa.

A wannan yanayin da ake ciki, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin aiwatar da manufofin samar da karin kasafin kudi, da na kudi da dai sauran manufofin tattalin arziki a jere, ciki har da manufar rage yawan harajin da aka buga wa kayayyakin da masana'antu ke samarwa, domin tabbatar da ganin tattalin arzikin kasar Sin ya samu isashen karfin tinkarar kalubaloli iri iri.

Ga misali, cikin farkon watanni 7 na bana, adadin darajar kayayyakin da kasar Sin ke shige da fice sun karu da kashi 4.2% bisa makamancin lokacin bara, lamarin da ya sheda cewa, manufar kasar Sin ta habaka hanyoyin ciniki, da samar da sauki ga harkoki masu alaka da cinikayya a kasar, ta yi amfani, don haka za a iya tinkarar illar da takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka ta haifar. Ban da haka, a cikin wadannan watanni 7 da suka wuce, kasar Sin ta samu damar yin amfani da karin jarin ketare, inda karuwar ta kai kashi 7.3%, yayin da karuwar jarin waje da ake samu a fannin sana'ar fasahohi masu zamani ta kai kashi 43.1% bisa makamancin lokacin bara. Hakan ya nuna cewa, kasar Sin tana kokarin kyautata muhallinta a fannin ciniki, da karfafa matakan kare hakkin mallakar fasaha, ta yadda kasar ta samu kare matsayinta na daya daga cikin kasashe mafi janyo jarin waje.

Ban da haka kuma, a cikin wadannan watanni 7 da suka gabata, kasar Sin ta fi samun karuwa a fannin harkar samar da kayayyaki masu ci gaba matuka, inda karuwar a wannan fanni ta fi karuwar sauran masana'antun kasar da kashi 2.9%, hakan ya nuna cewa, fasahohin zamani na kara zama ginshikin tattalin arzikin kasar. Haka zalika, a kowace rana a kan samu yin rajistar sabbin kamfanoni 19,600 a kasar Sin bisa matsakaicin matsayi, hakan yana nufin matakan da kasar ta dauka a kokarin taimakawa gudanar harkoki a kasuwanninta, suna sanya wa al'ummun kasar kaimi domin su kara kokarin bude kamfanoni, gami da kirkiro sabbin fasahohi, abin da ya kara ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.

Yanzu haka karuwar tattalin arzikin kasar Sin tana kan gaba cikin manyan rukunoni masu karfin tattalin arziki a duniya. Kasar ta Sin tana kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Ko da yake wasu masu mugun nufi sun yi hasashen cewa, tattalin arzikin Sin zai samu koma baya, amma ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya sanya hasashensu ya zama karya, kuma abin dariya.

Kwanan baya, mujallar Fortune ta kaddamar da jerin sunayen kamfanoni 500 mafi karfi a duniya, inda ta ce, yawan kamfanonin kasar Sin da ke cikin jerin sunayen a bana ya kai 129, wanda ya wuce na kasar Amurka karo na farko. Yadda kamfanonin kasar Sin suke kyautata karfinsu na yin takara a duniya. Ya nuna cewa, kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikinta. Kamar yadda kwararru masu ilmin harkokin kasar Sin na Amurka fiye da 200 suka bayyana cikin wata wasikar da suka aike da ita a fili tare da sanya hannu a kanta, sun ce, Amurka ba za ta iya hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba, kana ba za ta iya hana Sin ta fadada rabonta a kasuwannin kasa da kasa ba, kuma ba za ta iya hana kasar Sin ta kara taka muhimmiyar rawa a cikin al'amuran kasa da kasa ba.

Komai sauye-sauyen da za ta fuskanta a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, za ta tsaya kan zurfafa gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, sa'an nan za ta kara kyautata karfinta na jure wahala ta fuskar raya kasa. Tattalin arzikin kasar Sin zai samu bunkasa duk da matsalolin da ake fuskanta, kuma kasar Sin za ta samu amfanar kowa tare da kasashen duniya. (Sanusi, Bello, Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China