Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan makamashi da Sin ke samarwa ya karu da kaso 3 bisa dari a watanni 7 na farkon shekarar bana
2019-08-14 19:52:28        cri

Yawan makamashin lantarki da Sin ke samarwa ya karu da kaso 3 bisa dari a watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2019.

Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta kasar NBS ta fitar a Larabar nan, sun nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na bana, adadin lantarkin da kasar ta samar ya kai sa'aoin kilowatt tiriliyan 4.

Alkaluman sun nuna karuwar makamashin lantarkin kasar ta Sin, inda adadin da ake samu daga makamashin nukiliya ya karu da kaso 18.2 bisa dari, kana wanda ake samarwa daga hasken rana ya karu da kaso 13.2 bisa dari a shekara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China