Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Layin dogon da Sin ta gina ya hada gabobin tekun gabashi da yammacin Afirka
2019-08-13 11:14:12        cri

Kwanakin baya jirgin kasan jigilar fasinjoji masu bude ido kusan 50 na Rovos Rail ya tashi daga layin dogon Benguela na birnin Lobito dake bakin tekun kasar Angola zuwan Dar es Salaam, fadar mulkin kasar Tanzaniya, jirgin kasan shi ne na farko da ya tashi daga layin dogon zuwa birnin dake gabar tekun Indiya.

Layin dogon Benguela wanda kamfanin gina layin dogon kasar Sin ya gina, ya ratsa fadin kasar ta Angola, zai kuma hada layin dogon da aka gina tsakanin kasashen Tanzaniya da Zambiya a shekarun 1970, a don haka ba ma kawai layin dogon zai hada layukan dogo na kasashe hudu wadanda suka hada Tanzaniya da Zambiya da jamhuriyar domokuradiyar Congo da kuma Angola ba, har ma zai taimakawa ci gaban tattalin arziki da yawon shakatawa a yankunan dake gabobi biyunsa.

Domin tabbatar da jirgin kasa na kai koma a layin dogon yadda ya kamata, kamfanin gina layin dogon dake kasar ta Angola ya tura wasu kwararrun ma'aikata don koyon yadda ake tafiyar da harkokin da abin ya shafa zuwa yankunan dake gabobi biyu na layin dogon domin yin sintiri, ta yadda za a rika tafiyar da ayyukan jirgin cikin lumana.

Jose Gamoda, daya ne daga cikin ma'aikatan da kamfanin kasar Sin ya tura, kauyen sa yana da nisan mita sama da 100 ne kawai daga layin dogon Benguela, tun daga shekarar 2006 wato tun bayan da ya rasa aikin yi, ya fara yin aiki a sashen aikin gina layin dogon Benguela na kamfanin kasar Sin, kawo yanzu, ya shafe tsawon shekaru 13 yana aiki a kamfanin.

Bisa kokarin da ma'aikatan kasashen biyu wato Sin da Angola suka yi a cikin shekaru sama da goma da suka gabata, an kammala aikin gina layin dogon Benguela mai tsawon kilomita 1344 a watan Yulin shekarar 2017, daga baya an mika layin dogon ga gwamnatin wurin domin kaddamar da shi. Abu mai faranta rai shi ne tun bayan da layin dogon ya fara aiki, mazauna yankunan dake kusa da layin dogon sun amfana matuka, misali mazaunan kauyen Jose Gamoda su kan shiga jirgin kasa domin zuwa wurare daban daban.

Jose Gamoda ya gaya mana cewa, wurin da yake aiki yana kusa da gidansa, a don haka yana zuwa wurin aiki da wuri, kana abokan aikinsa da suka zo daga kasar Sin su ma suna da kirki, shi ya sa yana son ci gaba da aiki a kamfanin saboda yana jin dadin aiki matuka.

Mai kula da aikin kamfanin kasar Sin dake kasar Angola ya yi mana bayani cewa, layin dogon Benguela babban aiki ne a tarihin kasar Angola wanda ya kasance layin dogon zamani mafi tsayi a kasar, inda aka gina shi da ma'auni da fasaha da kayayyaki na kasar Sin, kana ya kasance layin dogo mafi tsayi da kamfanin kasar Sin ya gina a ketare a karnin nan da ake ciki.

Kididdigar da sashen kula da aikin jigilar fasinjoji na hukumar jirgin kasar Benguela ta nuna cewa, tun bayan da layin dogon ya fara aiki, kawo yanzu gaba daya adadin fasinjojin da aka jigilar su ta layin dogon ya kai kusan miliyan 4 da dubu 200, adadin kayayyakin da aka yi jigilar su ya kai tan dubu 290, kana layin dogon ya riga ya kasance muhimmiyar hanyar zuwa tasoshin gabar teku na kasashen jamhuriyar demokuradiyar Congo da Zambiya da sauransu, haka kuma ya rage kudin jigilar albarkatun ma'adinnai na kasashen yayin da suke fitar da albarkatun ma'adinnai zuwa kasashen waje. Ana iya cewa, layin dogon ya taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin yankunan dake kusa da shi da kuma musanyar kayayyaki tsakanin yankunan dake nesa da gabar teku da na gabar teku, zai kuma taimakawa birnin Lobito zama muhimmin birnin sufuri dake yankin yammacin nahiyar Afirka.

Hakika hukumomin yawon shakatawa da al'adu da sufuri na kasar Angola suna mai da hankali matuka kan jirgin kasar bude ido na Rovos Rail, sun mayar da shi a matsayin alamar zamanantar da aikin yawon shakatawa a kasar, wani jami'in da abin ya shafa ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ake amfanin da jirgin kasa na bude ido na Rovos Rail shi ne domin an gina layin dogon Benguela, wanda yake da babbar ma'ana wajen hada layukan kasa dake tsakanin kasashen Afirka baki daya, da kuma ci gaban aikin bude ido a yankunan dake kusa da layin dogon.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China