Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Hong Kong yankin kasar Sin ne da ba za a iya raba shi ba
2019-08-15 16:34:46        cri

A kwanakin baya ne, wasu matasa masu zanga-zanga suka tsare kofar ofishin wakilin gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake yankin Hong Kong, tare da bata tambarin kasa dake kofar ofishin da wasu launuka, matakin da kakakin ofishin kula da harkokin Hong Kong da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin ya yi tir da shi.

Jami'in ya ce, masu zanga-zangar sun yi wa ofishin tsinke, tare da bata bangonsa da wasu rubuce-rubuce na batanci, da kuma kokarin kutsa kai cikin ginin.

Hakan a cewar jami'in, mataki ne na kalubalantar ikon gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ya kuma keta hurumin ginshikin nan na "kasa daya, tsarin mulki biyu", wanda hakan babban al'amari ne dake nuna mummunan misali da ba za a lamunta ba.

Sai dai wasu kasashen duniya masu martaba doka sun yi zargi, da yin Allah wadai da ayyukan da masu ta da rikicin suka gudanar a yankin Hong Kong. Amma wasu jama'a a nahiyar Turai sun raina batun, inda suka mai da ayyukan a matsayin zanga-zangar lumana, tare da bukatar gwamnatin yankin Hong Kong da ta yi watsi da yankewa masu tayar da rikcikin hukunci, da kuma zargin 'yan sandan yankin, cewa sun yi amfani da karfin tuwo.

Amma a nata bangaren, gwamnatin tsakiya ta ce, tana goyon bayan gwamnatin yankin musamman na Hong kong da ta dauki mataki bisa doka wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro da wadata mai dorewa. Rundunar soja dake yankin tana martaba ka'idar yankin da dokar jibge soja, matakin da ya ba da tabbaci ga zaman lafiya da wadata mai dorewa a yankin。

A shekarar 2018 da ta gabata, an ayyana yankin a matsayin na 18 a duniya wajen gudanar da harkokinsa bisa doka, matakin da ya dara na kasar Amurka, wadda ke matsayi na 60 a duniya a shekarar 1996.

Yankin musannan na Hong Kong wani yanki ne na kasar Sin, kuma babu wata kasa, ko wata kungiya, ko ma daidaikun mutane da ke da ikon tsoma baki a cikin harkokinsa, ko raba shi daga kasar Sin. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China