Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kullum kasashen yamma na amfani da fuska biyu wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe
2019-07-30 14:37:14        cri

Tun a tsakiyar watan Yuni ne, wasu matasa suka fara ta da zaune tsaye a yankin musamman na Hongkong na kasar Sin. Wasu Turawa musamman daga kasshen Burtaniya da Amurka sun tashi haikan suna amfani da fuska biyu suna tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, inda suke zuga masu tsattsaura ra'ayi su yi amfani da karfin tuwo, da kuma yin Allah wadai da matakan da 'yan sandan yankin suka dauka na daidaita zanga-zangar baya-bayan da wasu matasa suka gudanar, suna zargin cewa, gwamnatin kasar Sin na ci gaba da take 'yanci da ma ikon da yankin ke da su, wannan karya ce da munafunci. Shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan kasar Amurka Eliot Engel ya yi ikirari a kwanan baya cewa, 'yan sandan yankin Hong Kong sun yi amfani da karfin tuwo kan matasan dake zanga-zanga a yankin, matakin da ya bata sunan Hongkong ta fuskar aiwatar da harkoki da doka na yankin, wadannan kalamai ko kadan ba su da tushe kuma ba su bayyana abin gaskiya da ke faruwa a yankin ba, kuma ko shakka babu wannan matakin sa hannu ne a harkokin cikin gidan sauran kasashe.

Wasu Turawa 'yan siyasa ciki hadda Eliot Engel na ganin cewa, matakan nuna karfin tuwo da aka dauka a yayin zanga-zangar da aka yi a kasashen yamma su ne laifin nuna karfin tuwo ne, kuma wadanda suka kai hari kan 'yan sanda su ne 'yan bore. Kana 'yan sanda nasu suna da ikon dakile irin wadannan masu zanga-zanga. Amma idan irin wannan laifi ya auku a yankin Hongkong, a ganinsu, ya zama zanga-zangar da ake yi cikin lumana. Har ma sun nemi gwamnatin yankin Hong Kong da ta mutunta 'yancin fadin albarkacin baki da na shirya zanga-zanga, har ma sun nemi gwamnatin yankin Hongkong da ta soke zargin da ta yi wa wadannan masu zanga-zanga wadanda suka aikata laifin keta doka. A ganinsu, masu nuna karfin tuwo na yankin Hongkong su ne "Jarumai dake tsaron hakkin Bil Adama da 'yanci". Matakin da Turawa 'yan siyasa kamar Eliot Engel suka dauka bisa fuskoki biyu ya alamta cewa, Turawa 'yan siyasa ba su sahihanci da da'a sai munafunci a zukatansu.

Ko wadannan Turawa sun manta, cewar 'yan sandan Amurka sun yi amfani da ruwan yaji da hayaki mai sa kwalla da harsasan roba kan masu zanga-zanga da suka "mamaye titin Wall Street" suka bayyana rashin dadinsu a shekarar 2011. Ban da wannan kuma, a wannan shekara, 'yan sandan Birtaniya sun yi amfani da mesan ruwa mai karfi don tarwatsa masu ta da zaune tsaye a London. Amma idan batun da ya shafi yankin Hongkong ne, wadannan 'yan siyasa na canja fuska, inda suka yi watsi da hakurin da 'yan sandan yankin suka yi lokacin da suka fuskanci takala da masu karfin tuwo suka yi musu, a maimako su yi tir da matakin da 'yan sanda suka aikata bisa doka ba gaira ba dalili.

A cikin shekaru 22 da suka gabata bayan dawowar yankin Hongkong karkashin shugabancin kasar Sin, gwamnatin tsakiyar kasar Sin tana nacewa ga aiwatar da tsarin "kasa daya, amma tsarin mulki biyu", "Mutanen Hongkong ne na gudanar da harkokin yankin da kansu" cikin 'yanci", bisa kundin tsarin mulkin kasar Sin da babbar dokar yankin musamman na Hongkong. Mutanen Hongkong na da cikakken ikon tafiyar harkokinsu cikin 'yanci. Rahotanni na cewa, a shekarar 2018 da ta gabata, an ayyana yankin a matsayin na 16 a duniya wajen gudanar da harkokinsa bisa doka, daga matsayi na 60 a duniya a shekarar 1996, matakin da ya dara na kasar Amurka. Wadannan Turawa 'yan siyasa wadanda suka yi karya yadda suke so, ko sun fahimci ko ba su fahimci mene ne doka da shari'a ko kadan?

Kafofin yada labarai na kasashen yamma su kan ayyana kansu a matsayin masu adalci da gaskiya, amma ba su watsa labaru kan yadda 'yan siyasarsu suka tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe kamar yadda ba su gani ba su sani ba. A cikin labaran da suka gabatar dangane da tashe-tashen hakula a Hongkong, ba su ambaci matakan takalar da masu zanga-zanga suka yi ba ko kadan, alal misali, a ran 14 ga wata, masu zanga-zanga sun ciji yatsan wani dan sandan yankin har sai ya cire, da kuma a ran 21 ga wata, inda masu zanga-zanga suka lalata tambarin kasar Sin, matakin da ba wata kasa mai cikakken 'yanci za ta lamunta, amma duk wadannan al'amura, wadannan kafofin yada labarai na yammacin duniya ba su mai da hankali a kansu ba ko kadan, ina adaci ko gaskiya a nan?

Tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe ba ma kawai ya sabawa dokar kasa da kasa ba, har ya keta tushen ka'idar dangantakar kasa da kasa. 'Yan siyasar Turawa sun yi amfani da fuska biyu don shisshigi harkokin cikin gida na sauran kasashe, wannan makirci ne. Ya zuwa yanzu, sun yi karya yadda suke so kan zanga-zanga da tashe-tashen hankalun da suka auku a Hongkong kwanan baya tare da kau da ido kan lamarin, har sun kara dagula halin da ake ciki a wurin, duk bisa mummunan burinsu na tada zaune tsaye a yankin, har za su yi amfani da shi wajen dakile babban yanki. Gwamnatin yankin musamman, 'yan sandan yanki da jama'ar yanki ba za su yarda wata kasa ko kungiya ko daidaikun mutane su kawo illa ga tushen gudanar da harkokin yankin bisa doka ba. Kana Sin ba za ta bar Hongkong cikin mawuyancin hali kamar yadda ya shiga a halin yanzu ba ko kadan, za ta yi iyakacin kokarin daukar matakan da suka dace don kiyaye 'yanci da wadata da zaman lafiya mai dorewa a yankin musamman na Hongkong na kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China