![]() |
|
2019-07-29 11:17:08 cri |
Jami'ai da wakilan kungiyoyin duniya da jagororin 'yan kasuwa da masana sama da 400 da suka zo daga kasashe fiye da 30 a fadin duniya sun yi musayar ra'ayoyi da juna bisa taken "kiyaye muhalli a sassan ziri daya da hanya daya da makomar bai daya ga dukkan bil Adam" da "daidaita matsalar kwararowar hamada da kara kudin shigar manoma da makiyaya" da sauransu, kan yadda za a yayata tsarin da ake amfani da shi a Kubuqi wajen magance matsalar kwararowar hamada.
Mahalarta taron suna ganin cewa, magance matsalar kwararowar hamada batu ne ya shafi moriyar 'yan Adam baki daya, kuma aiki ne ja wur da kuma girma. Masanan da abin ya shafa sun bayyana cewa, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa a fannin daidaita muhallin duniya, kuma tsarin da ake amfani da shi a Kubuqi wajen magance matsalar kwararowar hamada tsari ne mai kyau, kamata ya yi kasashen duniya su yi kokarin yin hadin gwiwa a fannin magance kwararowar hamada, don yayata tsarin ga karin kasashe da shiyyoyin da ke fuskantar irin wannan matsala. (Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China