Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai kamata a cire kasar Sin daga jerin kasashen dake tasowa ba
2019-07-28 17:33:44        cri

 

Fadar White House ta Amurka ta bukaci wakilin cinikayyar kasa da ya dauki duk wani matakin da ya wajaba domin yin kwaskwarima ga matsayin kasashen dake tasowa membobin kungiyar cinikayya ta duniya ko kuma WTO a takaice, da yin barazanar cewa, idan ba'a samu ci gaba cikin kwanaki casa'in ba, akwai yiwuwar Amurka ita kanda za ta dauki mataki. Wannan ya nuna irin babakeren da Amurka ke yi a duniya.

Sanin kowa ne, tantance matsayin kasashen dake tasowa a WTO abu ne da kungiyar ta dade tana yi domin taimakawa wadannan kasashe yin gyare-gyare a gida da bude kasuwanninsu ga duniya. Gatancin da aka nunawa kasashen dake tasowa a WTO na iya taimaka musu wajen bunkasa tattalin arziki, da aza tubali mai inganci ga tsarin kasuwancin duniya.

Amma duk da haka, kasar Amurka na ganin cewa hakan ya baiwa kasashen dake da saurin bunkasuwar tattalin arziki damar cin moriyarta, don haka ta dade tana bukatar a yi kwaskwarima. Bayan da kasar Sin ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya a shekara ta 2010, zuwa yanzu, kasar Amurka na kara bukatar a kebe kasar Sin daga cikin jerin kasashen dake tasowa a duniya.

 

 

Idan ana so a tantance wata kasa ta zama kasar dake tasowa ko kasa mai sukuni, bai kamata a yi la'akari da fanni guda daya kawai ba, ya zama dole a yi la'akari da fannoni daban-daban, ciki har da jimillar adadin tattalin arziki, da matsakaicin yawan GDP kan kowane dan kasa, da tsarin masana'antu, da karfin kirkire-kirkire da sauransu. Kasar Sin na da yawan jama'a kusan biliyan 1.4, amma matsakaicin GDPn kasar a kan kowane dan kasar bai kai dala dubu 10 ba, adadin da bai kai matsakaicin adadin duk duniya ba, har ma bai kai kaso daya bisa shida na Amurka ba. Har wa yau, akwai rashin daidaiton ci gaba tsakanin sassa daban-daban na kasar Sin, har ma akwai mutane sama da miliyan 16 wadanda ke fama da kangin talauci.

Bambancin dake kasancewa a tsakanin kasashen Sin da Amurka, shi ne gibin dake kasancewa a tsakanin wata kasa mai tasowa da ta fi girma a duniya da wata kasa mai ci gaba da ta fi girma a duniya. Don haka, idan kasar Amurka ta musunta matsayin kasar Sin na kasa mai tasowa bisa ma'aunin jimillar tattalin arziki kawai, to wannan ba ya da tushe.

A halin yanzu dai, wani abun na musamman na tsarin tattalin arzikin duniya shi ne, tasowar kasuwanni masu tasowa da kasashe masu tasowa, wadda ta taka muhimmiyar rawa kan gudanar da harkokin kasa da kasa. Kuma hakan ba ya saba da matsayinsu na mambobin kungiyar ta WTO.

A mako mai zuwa, za a shirya shawarwarin koli zagaye na 12 game da batun tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Amurka a birnin Shanghai na kasar Sin. Dalilan da suka sanya kasar Amurka ta zabi wannan lokaci don daukar matakin karawa kungiyar WTO matsin lamba, da nufin tilasta mata yin kwaskwarima kan matsayin mambobi kasashe masu tasowa, su ne ba kawai ka'idojin da kungiyar ke bi ba su iya biyan bukatun kasar Amurka ba, har ma ta yi yunkurin ci gaba da matsawa Sin lamba, hakan za ta iya kara gabatar da bukatunta a fannonin kiyaye ikon mallakar fasaha, da samun iznin shiga kasuwa da dai sauransu a gun shawarwarin da za a yi.

 

Amma, duk wane irin burin da kasar Amurka ke fatan cimmawa, akwai bukatar kasashen duniya su tattauna tare wajen tsara ka'idojin gudanar da harkokin duniya, amma ba bi umurni na wata kasa saboda karfin da take nunawa ba. Ko da yaushe kasar Sin na tsayawa kungiyar WTO wajen yin kwaskwarima, don kara karfin kungiyar na fada a ji, amma a waje guda kuma kasar Sin ta jaddada cewa, a yayin da ake yin kwaskwarimar, ya kamata a kiyaye babbar darajar tsarin cinikayya na bangarori da dama, da kiyaye moriyar mambobi masu tasowa, da kuma bin tsarin shirya manufofi irin na cimma ra'ayin bai daya. Kana kasar Sin tana son daukar nauyin dake dacewar matsayin ci gaban tattalin arzikinta da karfinta, kana za ta tsaya kan kiyaye iko da moriyar mambobi kasashe masu tasowa. Ko shakka babu kasar Sin za ta cika alkawarinta a fannin kiyaye babbar moriyar kasa da ta jama'a, duk wani irin matsin lamba da zamba ba za su iya kawo tasiri ga kasar Sin ba. (Bilki, Murtala)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China