Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Ya kamata kasar Amurka ta daidaita matsalarta ta hakkin bil Adama
2019-07-27 20:32:25        cri

A kwanakin baya, cibiyar nazarin batun hakkin bil Adama ta kasar Sin ta gabatar da wani rahoto mai taken " Matsalar kabilancin da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar Amurka ta nuna cewa, maganar kasar Amurka na kare hakkin dan Adam karya ce". A cikin rahoton, an ambaci rahotannin da wasu masanan kasar Amurka suka rubuta, da labarun da kafofin watsa labarun kasar suka watsa, gami da sakamakon nazarin da wasu kungiyoyin kasa da kasa suka yi. Wadannan batutuwa sun nuna yadda kasar Amurka ta dade tana fama da matsalar kabilanci, kana yadda kasar take kallon kanta wata kasa mai kare hakkin dan Adam, hakika karya ce kawai. Daga bisani za a gano cewa, 'yan siyasa na kasar Amurka suna yin amfani da maganar hakkin dan Adam wajen cimma burinsu na siyasa.

Kasar Amurka wata kasa ce mai kabilu daban daban, da al'ummu makaurata da yawa. Duk da cewa gwamnatin kasar ta dade tana kokarin yayata manufofinta na "Zaman gauraya da juna", da "Samun daidaituwa tsakanin daidaikon mutane", amma har yanzu ana fama da kabilanci mai tsanani, da samun rikice-rikice tsakanin al'ummun kasar, wanda ya riga ya zama wata babbar matsala mai alaka da hakkin dan Adam da aka kasa daidaitata a kasar. Idan an dubi tarihin kasar, ko kuma karanta jaridun kasar na yanzu, za a gane da cewa, munanan ayyukan take hakkin dan Adam na wasu kabilu ba su taba tsayawa ba. Har yanzu akwai wasu al'ummun kasar, wadanda ke zama cikin mawuyacin hali, a fannonin zaman rayuwarsu na neman aikin yi, da samun karin girma, da albashi, da damar samun ilimi, da jin dadin kayayyakin al'adu, da dai sauransu. Ban da haka kuma, a kan yi musu rashin adalci a fannin shari'a.

Ga misali, a shekarun baya, sau da yawa ana jin labarin cewa 'yan sandan kasar Amurka sun azabtar da wasu matasa na wasu al'ummun kasar, har ma an harbe su ba gaira ba dalili. Wannan batu gaskiya kusan ba a iya ganinsa a sauran kasashe daban daban. Amma a kasar Amurka, har yanzu ana maimaita wadannan aikace-aikace marasa adalci da tausayi cikin kiri da muzu.

Abun takaici shi ne, har zuwa yau, Amurka ba ta kyautata tunaninta na nuna bambancin launin fata ba bisa bunkasuwar zamani da al'umma, har ta kara habaka wannan tunani, matakin da ya kawo babbar illa ga tushen kasar. A halin yanzu da ake kokarin dunkule duniya waje guda, tunanin mai da fararen fata fiye da kowa da sanya kiyayya abin ban mamaki ne wanda bai dace da halin da muke ciki ba.

Mujallar "Time" ta yiwa kasar Amurka lakabi da kasar da ta samu baraka, bisa yin la'akari da alkaluman da hukumar bincike ta tarayyar Amurka ta bayar, alkaluman da suka nuna cewa, a shekarar 2017, yawan laifufukan nuna kiyayya da aka aikata a kasar ya karu da kashi 17 cikin dari bisa na makamancin lokaci na 2016, daga cikinsu laifufuka da aka aikata dangane da launin fata ya fi yawa. Kana an ce an fi aikata wadannan laifuffuka masu alaka da launin fata kan Amurkawa 'yan asalin Afirka da masu bin addinin Yahudawa sun fi fama da shi. Amma gwamnatin Amurka ba ta dauki ko wani matakin dakatar da wadannan laifuffuka ba, a maimakon haka kuma , wasu 'yan siyasa suna yunkurin habaka tunanin nuna bambancin launin fata da ra'ayi na nuna kyamar kwararru da fitattun mutane na wata al'umma.

A fadin duniya kuma, Amurka ta yi ta daga tutar "hakkin Bil Adam ya fi ikon kasa", inda kuma take hura wutar rikici a tsakanin al'ummomi daban daban, don cimma moriyar kanta, matakin da ya kawo matsaloli ga zaman lafiya a duniya. A sa'i daya kuma, ta janye jikinta daga hukumar kare hakkin bil Adam ta MDD da ma aikin daddale yarjejenyar kasa da kasa kan batun 'yan gudun hijira, ta kuma ki amincewa da yarjejeniyar kasa da kasa kan tattalin arziki da zaman al'umma da al'adu da yarjejeniyar hakkin yara da ma yarjejeniyar hakkin nakasassu.

A yayin da 'yan siyasar Amurka suka yi biris da mummunan halin da kasarsu ke ciki ta fannin hakkin bil Adam, kasar ta na kuma zargin kasashe kusan 200 da rashin kare hakkin bil Adam yadda ya kamata. Wani babban jami'in kasar a kwanakin baya ya soki kasar Sin kan manufofinta da suka shafi jihohin Xinjiang da Tibet da ma 'yancin addini.

Sai dai a jiya Jumma'a, jakadun wasu kasashe 50 sun rattaba hannu kan wata wasika da suka aikewa shugaban hukumar kare hakkin dan Adam da babbar kwamishinar dake kula da hakkokin dan Adam ta majalisar, inda suka bayyana goyon bayansu ga matsayar kasar Sin dangane da batun jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar, sun kuma yabawa Kasar Sin bisa nasarorinta a fannin tattalin arziki, da zaman takewa, da ingantacciyar hanyar yaki da ta'addanci, da matakan kawar da tsattsauran ra'ayi, da kuma tabbatar da hakkin dan Adam. Matakin da ya kasance mayar da martani game da yadda 'yan siyasar Amurka ke yi wa kasar Sin bakin fenti.

'Yan siyasa na Amurka suna ta kara ba wa al'umma dariya bisa ga yadda kasar ke amfani da hakkin bil Adam wajen kare babakeren da ta yi a duniya, a yayin da kuma take yin ko oho da halin da take ciki. A gabanin matsalolinta na nuna bambancin kabilu da jinsuna da karuwar gibi tsakanin matalauta da mawadata, ya kamata kasar Amurka ta daidaita matsalarta da farko.(Masu fassara:Bello Wang, Amina Xu, Lubabatu Lei, dukkansu ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China