Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta himmantu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya
2019-07-26 20:31:50        cri
Babbar kanar a tawagar kasar Sin a kungiyar tarayyar Afirka (AU) Wang Ximao, ya bayyana kudirin kasarsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaron duniya da ma taimakawa kokarin Afirka a wannan fanni.

Wang ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, yayin da yake jawabi a wajen wata liyafa da tawagar ta shirya don murnar cika shekaru 92 da kafa rundunar sojan kwatar 'yancin kasar Sin (PLA), yana mai cewa, rundunar PLA ta shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, da ayyukan yaki da 'yan fashin teku da shiga ayyukan ceto da taimakon jin kai na kasa da kasa.

Ya ce, a 'yan shekarun da suka gabata, rundunar PLA ta shiga ayyukan kiyaye zaman kafiya na MDD har sau 24, sau 16 daga cikinsu a nahiyar Afirka, kana daga cikin dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya 39,000 da kasar Sin ta tura, 32,000 an tura su ne nahiyar Afirka. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China