Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojan kasar Sin na ba da babban taimako ga shimfida zaman lafiya a duniya
2019-07-25 13:03:58        cri


Gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken tsaron kasa a sabon zamanin da ake ciki jiya Laraba, inda ta bayyana manufofin tsaron kasar daga wasu muhimman fannoni shida, da nunawa duniya manyan tsare-tsaren inganta tsaron kasa da gina rundunar sojan kasar, tare da irin yakinin da rundunar sojan kasar Sin ke da shi. Karon farko takardar bayani ta ayyana sabuwar sigar musamman ta harkokin tsaron kasa na Sin, wato Sin ba za ta taba neman yin kama-karya ko fadada tasirinta a wasu sassa ba, wanda hakan shi ma jigo ne na manufofin kasar game da ayyukan soji a sabon zamanin da ake ciki.

Kasar Sin ta dade tana mai da "tsaron kai" a matsayin jigo na manufofinta ta fannin tsaro. A 'yan shekarun nan, kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen zurfafa yin gyare-gyare ga harkokin tsaron kasa da na rundunar sojanta, al'amarin da ya samu babbar nasara.

A halin yanzu kasar Sin na cikin wani muhimmin lokaci na neman bunkasuwa kana tana fuskantar barazana gami da kalubalen tsaro da dama. Duba da sauyawar halin da ake ciki a duk fadin duniya, Sin ta yi kokarin daidaita manufofinta na tsaro da kawo kwaskwarima ga ayyukan sojinta. Amma duk da haka, za ta ci gaba da maida "tsaron kai" a matsayin jigon manufofinta na tsaro, wanda ya nuna al'adun gargajiya mafi nagarta dake la'akari da zaman lafiya da lumana a matsayin jigo.

Kazalika takardar ta jaddada babban burin kasar Sin na inganta harkokin tsaron kasa, wato kare 'yancin mulkin kai, da tsaro da ci gaban al'umma. Har wa yau Sin ba za ta taba neman yin babakere, ko fadada tasirinta a wasu sassan duniya ba, wanda hakan shi ma jigo ne na manufofin kasar game da ayyukan soji a sabon zamanin da ake ciki.

Bugu da kari, karon farko takardar bayanin ta bayyana cewa, gina al'ummu masu kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama na da babbar ma'ana ga duk duniya, wanda ya nuna irin alaka ta kut da kut tsakanin inganta harkokin tsaron kasa da gina rundunar sojan kasar Sin da ayyukan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya. Hakan ya shaida cewa Sin na daukar nauyin dake rataye a wuyanta, kuma kasar Sin na maida "bautawa al'umma" muhimmin fanni cikin ayyukan tsaronta, har ma tana bautawa daukacin al'ummar duniya, abun da ya nuna cewa Sin babbar kasa ce dake tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Kazalika, takardar bayanin ta bayyana komai ga jama'a ba tare da wata rufa-rufa ba. Alal misali, takardar bayanin ta yi amfani da dimbin alkaluma da kididdiga don bayyanawa duniya yadda kasar Sin ta yi amfani da kudadenta ta fannin tsaron kasa, inda ta yi nuni da cewa, yawan kudin tsaron kasa da Sin ta kashe a cikin jimillar alkaluman GDP gami da kasafin kudin kasar, da matsakaicin kudin tsaron kasar kan kowane dan kasar, duk ba su kai na wasu manyan kasashen duniya ba a shekara ta 2017. Wannan ya shaida cewa, kasar Sin na kokarin raya ayyukan sojanta domin tsaron kanta kawai, shi ya sa kalaman da wasu kasashen duniya suka yi cewa wai Sin na kawo barazana ga duniya ba su da gaskiya balle makama.

Kazalika, takardar bayanin ta nuna ire-iren sojojin da kasar Sin ke da su bayan da ta yi kwaskwarima ga rundunar sojanta, da manuofi da matakai da nasarori gami da babban burin rundunar sojan kasar, ciki har da sake jaddada shugabancin rundunar soja, da kyautata tsari, da raya harkokin tsaron kasa da gina rundunar sojan kasar daga dukkan fannoni. Takardar ta kuma yi bayani ga wasu muhimman batutuwan da suka ja hankalin duniya, ciki har da gina sansanin samar da tallafin soja a kasar Djibouti, da raya tsibirai a tekun kudancin kasar Sin, da raya sabbin makamai da sauransu. Har ma takardar bayanin ta jaddada kudurin gwamnatin kasar Sin na yaki da ayyukan cin hanci da karbar toshiya bisa doka, wanda ya shaida irin sahihanci gami da yakinin da rundunar sojan kasar Sin ke da shi. Babu tantama, sabuwar rundunar sojan kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, za ta dada bada babban taimako ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya baki daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China