Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ayyukan gona na zamani sun taimaka ga farfado da kauyuka a lardin Guangdong
2019-07-23 15:10:56        cri


Yanzu haka idan kuka je gandun noman shinkafa da ke birnin Huizhou na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin, za ku tarar da gonakin shinkafa a shimfide, kuma sauran kwanaki kadan suka rage a fara girbinsu. A cikin gandun, wakiliyarmu Lubabatu ta gamu da wani manomi mai suna Chen Youpeng, wanda fuskarsa ta haskaka da farin ciki, inda ya bayyana mata cewa, gonarsa za ta iya fitar da shinkafar da ta kai kimanin kilogram 2100 kan fadin kowane eka.

Chen Youpeng manomi ne da ke hadin gwiwa da kamfanin ayyukan noma na Haina da ke lardin Guangdong, wanda ke gudanar da wannan gundun noma tare da sauran wasu kamfanoni. Yana aikin kula da gonakin da suka kai fadin eka 50 a cikin gandun tare da uwargidansa, aikin dake ba shi kudin shiga Yuan (kudin Sin) sama da dubu 100 a kowace shekara. Ya ce, hakan ya fi yadda yake fita ci rani a baya. "Da farkon zuwanmu nan, muna cikin matsanancin talauci. Ga shi yanzu, yarana duka sun yi aure, kuma mun gina gidajenmu."

Li Weiting, shi ma manomi ne da ke hadin gwiwa da kamfanin Haina, ya ce, ya yi ta fita ci rani a baya, daga baya ya koma domin kulawa da yara a gida. A lokacin kuma, kamfanin Haina ya dauke shi aikin kiwon kifi a cikin gonakin shinkafa na kamfanin, yanzu kuma yana kiwon kifaye kimanin dubu 300 a cikin gonakin da suka kai eka 100. Ya kara da cewa, kamfanin ne yake ba da dukkanin kudin da ake bukata wajen kiwon, yana kuma ba shi albashin da ya kai yuan dubu 5 a kowane wata. Baya ga haka, kamfanin ya kan kuma raba kaso 20% na ribar da aka samu daga kiwon kifin. Ya ce, shi ma ya taba noma a gonarsa, sai dai bai iya samun kudi ba duk da cewa yana wahalar aiki. Amma yanzu ya samu tabbacin rayuwa, har ma ya sayi mota. Ya ce, hakan ya faru ne a sakamakon tsari na zamani da kamfanin yake bi. Ya ce, "Wannan tsarin da kamfanin yake bi ya samu karbuwa a wurina, sabo da babu lokacin hutu ga gonakin. Idan aka girbe shinkafa, za mu zuba ruwa a cikin gona don kiwon kifi. A lokacin hunturu kuma, idan aka gama girbin shinkafa, za mu kara zuba ruwa don kiwon kifi."

Tsarin da ke bakin manomi Li Weiting shi ne tsarin noma na zamani da kamfanin Haina ya dauka wanda ya hada ayyukan shuka da na kiwo a gu daya. A cikin gonakin kamfanin, ban da shinkafa, akwai kuma kifi da agwagi da kwadi da kuma kunkuru da ake kiwo, wadanda suke iya cin ciyayi da ma kwari masu illa a cikin gonakin, a yayin da kashinsu ke iya inganta gonakin. A wani bangaren na gonakin kuma, an shuka bishiyoyin da ke fid da 'ya'ya, kuma a nan ma, ana kiwon agwagi a karkashinsu.

Malam Zhong Zhenfang, babban darektan kamfanin Haina ya ce, wannan tsarin da ake bi ya kara ribar da ake samu, ribar da za ta iya kai wa sama da yuan dubu 60 a fadin kowane eka, adadin da ya ninka fiye da sau daya. Zhong Zhenfang ya kara da cewa, noma na zamani ya bambanta da irin yadda manoma suka saba yi a lokacin gargajiya, noma na zamani na matukar dogara ga fasaha da kimiyya.

A hakika, kamfanin Haina ya dade yana hada gwiwa tare da cibiyoyin nazarin noma da dama, a shekarar 2017 kuma, ya kafa cibiyar nazari ta kansa. Malam Lu Huazhong kuma yana daya daga cikin manyan masana na kamfanin. Malam Lu Huazhong shi ne kuma shugaban kwalejin nazarin kimiyyar noma na lardin Guangdong, kuma ya bayyana cewa, "Muna hadin gwiwa ne da cibiyoyin nazari da dama, ciki kuwa har da kwalejin nazarin kimiyyar noma ta lardin Guangdong, da jami'ar koyon harkokin noma ta kudancin kasar Sin da jami'ar Zhongshan da sashen nazarin kasa na birnin Nanjing karkashin kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin da sauransu. Ban da haka, kamfanin Haina shi ma ya kafa cibiyar nazarin ayyukan gona. Kwalejinmu na tura wasu masana da daliban da suka samu digiri na uku su zo nan, don su ba da tallafi ta bangaren kimiyya. Tallafin da muke bayarwa na shafar fannoni da dama, ciki har da yayata sabbin fasahohi da ma sabbin irrai da muka fitar."

Malam Lu Huazhong ya kara da cewa, ba ma kawai sabbin fasahohi da tsarin noma suke bayyana alakar da ke tsakanin kimiyya da ayyukan noma na zamani ba, hatta ma ta fannin jerin ayyukan da aka alakantasu da ayyukan gona, ya ce, "Gandun noma na zamani yana dora muhimmanci a kan hada sana'o'i daban daban, wato na farko akwai ayyukan gona, inda bisa ga taimakonmu, kamfanin Haina ya samu fasahar noma mai inganci. Na biyu kuma shi ne sarrafa shinkafar da aka fitar, inda ban da shinkafa, muna kuma sarrafa nau'o'in kayayyaki da shinkafar. Na uku kuma shi ne, hada ayyukan gona da yawon shakatawa, wato mu mai da gona ta zama lambu, don mazauna birni su zo su shakata, kuma su gane wa idanunsu yadda muke noma, baya ga fadakarwa, za su kuma kara amincewa da kayayyakin da muka fitar."

A hakika, gandun noman na birnin daya ne kawai daga cikin irin gandayen noma na zamani na lardin Guangdong. Lardin Guangdong ya mai da raya irin gandaye a matsayin muhimmiyar hanya ta aiwatar da manufar farfado da kauyuka, kuma tun daga shekarar 2018, ya fara aiwatar da shirin kafa gandaye kimanin 150 a fadin lardin, kawo yanzu kuma an amince da 100 daga cikinsu. Ta wannan hanya kuma, ake fatan ganin kara inganta farfado da kauyuka tare da inganta ayyukan noma.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China