Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin ta kama sabuwar hanyar neman ci gaba
2019-07-22 20:15:54        cri

Da misalin karfe 9 da rabi na safiyar yau Litinin agogon, an kaddamar da shafin hada-hadar hannayen jari na kamfanonin kirkiro sabbin fasahohin zamani na kasar Sin wato STAR Market a kasuwar hannayen jari ta Shangahai, inda a kashin farko ta fara da kamfanoni 25. Sakamakon haka, kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin ta kama sabuwar hanyar neman ci gaba.

A yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare da aka shirya karo na farko a watan Nuwamban bara a Shanghai, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shelar cewa, za a kafa shafin hada-hadar hannayen jari na kamfanonin kirkiro sabbin fasahohin zamani, wato STAR Market a takaice da kaddamar da rejistar sayen hannun jari, inda cikin kwanaki dari 2 da wani abu kawai aka share fagen shafin STAR Market. Ba ma kawai lamarin ya biya bukatun wasu kamfanonin kirkiro sabbin fasahohin zamani na kasar Sin suke cikin gaggawa ba, har ma ya bayyana niyya da kokari na kasar Sin wajen hanzarta yin kwaskwarimar kasuwar hada-hadar kudi.

Da ma a lokacin da aka yi shirin kaddamar da bangaren da ya shafi kimiyya da kirkiro sabbin fasahohin zamani, an tabbatar da inda za a gwada yin gyare-gyare kan kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin. Wannan bangaren da aka kafa, za a gwada sabon tsari na gabatar da sabon hannun jari, inda za a yi rajista da sabuwar takardar hannun jarin kamfani a kasuwar hannayen jari, sa'an nan a yada wannan labari, daga bisani za a iya fara sayen takardun hannun jari a kasuwa. Wato ba sai an bi wasu matakai sa'an nan a kaddamar da takardar ba, kamar yadda tsarin IPO ya tanada a baya. A nan kamfanoni za su samu riba bisa halin da kasuwa ta kaya.

Ana bukatar ci gaban kasuwar jari ne domin taimakawa raya masana'antu. Ko da yake tattalin arzikin kasar Sin yana karuwa cikin sauri ba tare da wata tangarda ba, amma yana kara fuskantar yanayi na rashin tabbas. Saboda haka ana amfani da sabon bangaren da aka kebe na kimiyya da kirkiro sabbin fasahohin zamani, don gudanar da wasu gyare-gyare na gwaji a fannin kasuwar hada-hadar kudi, ta yadda za a janyo karin jari ga kamfanonin kirkiro sabbin fasahohin zamani, don taimaka musu raya sabbin fasahohi, da yin takara da sauran kamfanoni. Ta wannan hanya, za a samu damar kara zamanintar da masana'antu, da raya sabon nau'in tattalin arziki a kasar Sin.

Fara yin amfani da kasuwar cinikin takardun hannun jarin kamfanonin kirkiro sabbin fasahohin zamani, wani matakin da Sin take dauka na zurfafa yin kwaskwarima da habaka bude kofa ga kasashen waje, wanda kuma ya shaida gwazo da imani da kuma matakan da Sin take dauka a wannan fanni. A hakika, tun lokacin da aka gabatar da matakai guda 9 na bude kasuwar hada-hadar kudi ga ketare a ran 13 ga watan Yuni, ranar da aka bude wannan kasuwa, zuwa lokacin da aka gabatar da matakai guda 11 na bude kofar sana'ar hada-hadar kudi ga ketare a ran 20 watan Yuli, ranar da aka fara yin amfani da wannan kasuwa, Sin tana kara kokarinta na bude kofarta ga ketare.

Duk da cewa kasuwar ta kankama a rana ta farko da fara yin amfani da ita, amma akwai bukatar kara fahimta da yin hakuri ta yadda za ta gudana yadda ya kamata nan gaba. A matsayinta na kasuwar kudi mai cike da kuzari da makoma mai kyau da kuma inganci, za ta zama kafar gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai inganci. (Sanusi, Bello, Amina)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China