Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manhaja ta taimaka wa gwamnatin Sin wajen ba da hidimomin da ke shafar zaman rayuwar jama'a
2019-07-22 15:16:42        cri

"Lallai wannan manhaja ta saukaka aikin ba da hidima gare mu, wato wadanda ke da bukata ta musamman, lamarin da ya rage mana yawan lokuta, ta yadda babu bukatar mu rika zuwa nan da can sau da yawa. Gaskiya ta samar mana da sauki sosai."

Su Liping ce ta fada wa wakiliyarmu da kalaman, wadda ke zaune a birnin Shenzhen na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Bugu da kari, Madam Su ta furta cewa, tana da nakasa a kafarta, takardarta ta shaida matsayinta ta wadda ke da bukatar musamman ta bace a bara. Ganin yadda ta kan yi amfani da takardar a zaman yau da kullum, don haka bacewarta ta ba ta wahala sosai. Yayin da take damuwa kan batun, wata manhaja mai suna "Yueshengshi" tana ba da taimako. Ta ce,

"Wasu abokaina wadanda su ma masu bukatar musamman ne sun fada min cewa, akwai wata manhaja da ake gwadawa. Kuma sun koya min yadda ake amfani da ita. Gaskiya dai ba wuya ko kadan wajen amfani da ita, kuma cikin kankanen lokaci, na samu takardar tawa."

Madam Su Liping ta kuma bayyana cewa, bayan da aka yi amfani da manhajar a kan wayar salula, to bayan mako guda kacal ta sake samun sabuwar takardarta, wanda kullum ake bukatar a kalla wata guda a baya. Ban da wannan kuma, a da ake bukatar zuwa unguwoyi da hukumomin gwamnati da abun ya shafa sau da dama, domin gabatar da takardun da ake bukata, amma a halin yanzu, muddin an yi amfani da manhajar a kan wayar salula, to za a iya kammala dukkan ayyukan, lamarin da ya ba da sauki ga Madam Su Liping da sauran wadanda ke da bukata ta musamman.

Babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da tsarin "kara karfin kasar Sin ta hanyar raya ayyukan Intanet" a yayin babban taron karo na 19 na wakilan jami'yyar da aka kira a shekarar 2017, lamarin da ya sa kaimi ga tafiyar da harkokin gwamnati bisa fasahohin zamani. Manhajar "Yueshengshi" wani muhimmin sakamako ne da gwamnatin lardin Guangdong ta samu, wajen yin gyare-gyare ga yadda ake tafiyar da harkokinta bisa fasahar zamani. Manhajar ta hada albarkatun da suka shafi tsaron jama'a, da harkokin jama'a, da 'yan kwadago, da ba da tabbaci ga zaman al'umma, da ma ba da ilmi, a kokarin kara saurin warware matsalolin da jama'a ke fuskanta.

Shugaban kamfanin raya ayyukan Intanet na Guangdong Wang Xinhui, wanda ke kula da aikin kirkirar manhajar "Yueshengshi" ta bayyana cewa, an kirkira manhajar ce domin daidaita batutuwan da ke jawo hankalin jama'a. Wang ya kara da cewa,

"Aikin manhajar tamu shi ne ba da sauki ga ayyukan da suka shafi jin dadin jama'a, don haka muna dora muhimmanci sosai ga batutuwan da ke jawon hankalin jama'a. Yayin da muke kirkirar manhajar, mun yin bincike na tsawon watanni biyu domin fahimtar bukatun jama'a. Don haka, ayyukan karon farko da muka sanya cikin manhajar su ne wadanda ke da nasaba sosai ga zaman rayuwar jama'a, kamar takardun lasisi, da duba kudin da gwammati ta adana cikin katin jama'a wajen sayen gida, da dai sauransu."

Ra'ayin "mai da hankali kan abubuwan da jama'a ke lura a kai" ya sa manhajar "Yueshengshi" ta samu yawan masu yin rajista wajen amfani da ita cikin sauri. Ya zuwa yanzu dai adadin ya kai miliyan 13.17, yayin da matsakaicin yawan wadanda ke amfani da manhajar a ko wace rana ya kai miliyan 9.15. Mataimakin shugaban hukumar kula da kididdigar hidimomin ayyukan gwamnati ta lardin Guangdong Gao Shangsheng, ya furta cewa,

"matsakaicin wadanda ke amfani da manhajar a ko wace rana ya zarce miliyan 9. Bisa kididdigar ana iya ganin cewa, manhajar na samu karbuwa sosai. Guangdong na da al'umma fiye da miliyan 100, mene ne ma'anar miliyan 13? Wato akwai mutum daya cikin ko wane mutum 8 da ke amfani da manhajar 'Yueshengshi' a lardin mu. Gaskiya dai, wannan wani kyakkyawan labari ne, wanda ke nufin cewa, jama'a na so mu yi amfani da fasahar zamani wajen kyautata zaman rayuwarsu. Muna aiwatar da ayyukanmu bisa ra'ayin mai da batun jama'a a gaban kome."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China