Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin jirgin saman British Airways ya dakatar da sauka a Alkahira na tsawon mako guda
2019-07-21 16:46:34        cri

Kamfanin jirgin sama na British Airways ya sanar a yammacin ranar Asabar cewa ya dakatar da sauka da tashin jiragensa a birnin Alkahira na tsawon kwanaki 7.

An wallafa sanarwar ne a shafin intanet na kamfanin jiragen, an dauki matakin dakatar da zirga-zirgar jiragen ne domin samun damar yin wasu bincike.

Sai dai ba'a bada cikakken bayani game da daukar wannan matakin ba.

Amma sai dai shafin intanet na gwamnatin Birtaniya game batun masu zirga-zirga na kasa da kasa, ya bada shawara cewa, ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya tana shawartar masu zirga-zirga a shiyyar arewacin Sinai, sakamakon cigaba da ayyukan ba ta gari da hare-haren ta'addanci kan jami'an 'yan sanda da jami'an tsaro cewa hakan na iya haddasa hasarar rayuka.

Shawarar da aka sabunta a ranar Asabar ta nuna cewa, akwai yiwuwar 'yan ta'adda za su iya kaddamar da hari a Masar. Koda yake, mafi yawan hare-haren a arewacin Sinai ne, akwai barazanar yiwuwar hare-haren ta'addanci a duk fadin kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China