Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu jami'an siyasa na Amurka ba su da iznin yin magana game da bin addinai cikin 'yanci ba
2019-07-20 18:59:19        cri

Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo sun yi jawabai a ranar 18 ga wata, inda suka zargi kasar Sin da hana jama'a bin addini cikin 'yanci da keta hakkinsu na dan Adam. A matsayin manyan jami'an kasar Amurka, sun bayar da ra'ayoyinsu ba tare da shaida ba, kuma manufarsu ita ce tsoma baki ciki harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar dauko batun bin addini da tabbatar da hakkin dan Adam, da kuma tada rikici da rarrabuwar kawuna ga kasar Sin. ko shakka babu, hakan zai kawo illa ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Wasu mutanen Amurka sun fi son yin amfani da batun yankin Xinjiang da yankin Tibet wajen zargin manufofin Sin kan kabilu da addini. A cikin jawaban Pence da Pompeo, sun bayyana cibiyar ba da ilmi da horar da kwararru ta yankin Xinjiang a matsayin sansanin kara ba da ilmi ga masu tsattsauran ra'ayi na yankin, da kuma zargin Sin da tilasta masu bin addinin Buddha na yankin Tibet. Dukkansu biyu makafi ne wadanda ba su ga hakikkanin yanayin Sin da kasa da kasa suka amince ba.

A yankin Xinjiang, yawan masallatai ya kai dubu 24 da dari 400, kana gwamnatin yankin ta kafa cibiyar ba da ilmi da horar da kwararru, inda aka koyar da ilmi a fannonin harsuna, da dokoki, da fasahohi, da tunanin kawar da tsattsauran ra'ayi don ba da ilmi ga mutanen da suka aikata kananan laifuffuka, da kuma yin kokarin kawar da ayyukan ta'addanci kafin su faru. Ya zuwa yanzu, ba a samu kowane aikin ta'addanci ba har na tsawon shekaru 3 a yankin Xinjiang, wannan ya shaida cewa, matakan magance ta'addanci kamar kafa cibiyar ba da ilmi da horar da kwararru suna da amfani da kuma biyan bukatun jama'ar yankin.

A yankin Tibet, yawan wuraren addini ya kai fiye da 1700, mabiya addini dake wuraren sun kai fiye da dubu 46, kana an kafa kwalejin ilmin addinin Buddha na yankin Tibet, da dora muhimmanci da tabbatar da tsarin addinin Lama da littattafansu, hakan ya shaida cewa, jama'ar yankin Tibet suna da ikon bin addini cikin 'yanci bisa tsarin mulkin kasar Sin.

A shekarun baya bayan nan, wasu jami'an diplomasiyya na kasashen duniya da dama sun kai ziyara yankin Xinjiang da yankin Tibet tare da yin bincike, suna ganin cewa, gwamnatin kasar Sin ta gudanar da ayyuka da dama wajen tabbatar da hakkin dan Adam, musamman hakkin dan Adam na kananan kabilun kasar. Wasu mutanen kasar Amurka ba su zo yankin Xinjiang da na Tibet ba, amma suna raina yanayin bin addini da tabbatar da hakkin dan Adam da ake ciki a yankunan biyu, da yin watsi da ra'ayoyin kasa da kasa, suna kokarin ba da karya kan batun don cimma burinsu na siyasa.

Abin mafi muhimmanci shi ne, Sin ta tabbatar da ikon jama'a na bin addini cikin 'yanci bisa tsarin mulkin kasar, amma ba ta amince wani mutum ya kawo illa ga tsarin zamantakewar al'umma, da lafiyar jama'a, da tsarin ba da ilmi na kasar ta hanyar addini ba. Sin ta ki amincewa ayyukan sabawa tsarin mulki da dokokin kasar da wasu kungiyoyi ko mutanen kasashen waje suka gudanar ta hanyar addini, tare da yanke musu hukunci bisa dokoki. Wannan ne aikin da ya kamata kowace kasa ta yi bisa dokoki.

Amma wasu mutanen kasar Amurka sun dauki wani ra'ayi na daban dangane da batun tabbatar da hakkin dan Adam a kasar Sin da ya sabawa na sauran sassan duniya da kuma daukar matakan Sin na yanke hukunci ga masu aikata laifuffuka ta hanyar addini a matsayin matsawa mabiyan addini, har ma sun gana da wasu masu aikata laifuffuka a fili don nuna goyon bayansu da tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin. Hakan zai kawo illa ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da mutuncin kasar Amurka da kuma moriyarta gaba daya.

Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka ya dace da moriyar jama'arsu. Ya kamata manyan jami'an kasar Amurka kamarsu Pence da Pompeo su kara gudanar da ayyukan sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Idan ba su canja ra'ayoyinsu ba, to zai kawo illa ga mutuncinsu a tarihi. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China