Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai kamata ba kasashen Turai su nuna alamar da ba ta dace ba kan batun Hong Kong
2019-07-19 19:22:44        cri

Jiya Alhamis majalisar dokokin kasashen Turai, ta zartas da wani kudurin dake shafar batun Hong Kong, inda ta bukaci gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da ta soke karar da ta kai kan masu zanga-zanga, kuma ta gudanar da bincike kan aikin 'yan sandan yankin, kudurin ya kasa kula da tashe-tashen hankulan da suka faru a Hong Kong a cikin makwannin baya bayan nan, haka kuma ya yi biris da cin zarafin da masu zanga zanga suka yi wa 'yan sandan yankin. A bayyane ana iya lura cewa, majalisar dokokin kasashen Turai ta zartas da kudurin ne ba bisa ka'ida ba, kuma hakan babbar takala ce ga tsarin doka na Hong Kong, kuma kudurin tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, a don haka kasar Sin ta yi suka da kakkausar murya kan kudurin, kuma tana adawa da shi.

Gudanar da harkokin yankin Hong Kong bisa doka, tushe ne na tabbatar da kwanciyar hankali a yankin, kuma kafin makwannin da suka gabata, wasu masu tsattsauren ra'ayi a Hong Kong, sun kutsa kai a cikin harabar majalisar dokokin yankin, kuma sun ratsa hanya, suka kai hari ga 'yan sanda. Masu tsattsauren ra'ayin sun nuna karfin tuwon bisa shirin da suka tsara kafin lokaci, inda suka haifar da barazana ga kwanicyar hankali, da tsarin doka da oda a yankin, kana sun kawo barazana a fili ga tsarin "kasa daya da tsarin mulki iri biyu". Don haka ba zai yiwu wata kasa mai 'yancin mulkin kan ta, ta amince da hakan ba.

Kasa da kasa sun zargi, da yin Allah wadai da ayyukan da masu tada rikici suka gudanar a yankin Hong Kong. Amma wasu mutanen dake nahiyar Turai sun raina batun, da maida ayyukan a matsayin zanga-zangar lumana, tare da bukatar gwamnatin yankin Hong Kong da ta yi watsi da yanke hukunci ga masu tada rikicin, da kuma zargin 'yan sandan yankin, cewa sun yi amfani da karfin tuwo.

Wannan dai tamkar daukar ma'auni biyu ne kan rikicin, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa, da ka'idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Bisa hakan, an shaida ra'ayin Turai game da kokarin warware matsaloli ba bisa dokoki ba.

A cikin shekaru 22, tun bayan da Sin ta mayar da samun ikon mulkin yankin Hong Kong, gwamnatin kasar Sin ta bi tsarin mulki da dokokin yankin, da gudanar da ayyuka bisa tsarin kasa daya amma da tsari biyu, inda 'yan Hong Kong ke sarrafa harkokin yankin da kansu, ta hakan jama'ar yankin suna iya aiwatar da harkokinsu da kansu, da kuma samun karin ikon demokuradiyya da 'yanci.

Abin da ya kamata a lura shi ne, "kasa daya" ita ce tushen kasancewar "tsarin mulki biyu". Kamar yadda Sinawa su kan ce, idan babu gindin bishiya mai inganci sai babu yawan ganyayenta. 'Yan majalisar Turai sun yi zargin yadda gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ke tafiyar da harkokin yankin Hong Kong, da "tsoma baki" da Sin ta yi. Gaskiya dai, lamarin ya kyale wani hakikanin batu, wato kasancewar harkokin Hong Kong harkokin cikin gida ne na kasar Sin, wanda ya kasance kamar kashin kaji ne suke son shafawa kasar Sin.

Hong Kong wani yanki ne na kasar Sin, ko kadan babu wata kasa, ko wata kungiya, ko ma daidaikun mutane da ke da ikon tsoma baki a kan harkokinta. Dangantakar kud ta kud a tsakanin Sin da Turai, ta dace muradun bangarorin biyu, don haka ya kamata Turai ta kula da harkoki kanta, ta kuma dauki matakan a zo a gani wajen hadin kai tare da Sin, a kokarin ciyar da dangantakar su gaba. (Masu Fassara: Jamila, Zainab, Kande daga sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China