Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta gwada allurar riga kafin HIV da zai yi dogon tasiri
2019-07-19 15:56:07        cri
Babban mai binciken cutar kanjamau dake cibiyar yaki da riga kafin cututtaka ta kasar Sin Shao Yiming, ya bayyana cewa, masanan kasar za su fara kashi na biyu na gwajin allurar riga kafin cutar kanjamau kan mutane 160 da suka yarda a gwada maganin a jikinsu.

Jaridar China Daily ta wallafa a yau Jumma'a cewa, allurar mai suna DNA-rTV, tana mayar da hankali wajen rubanya kwayoyin halittar gadon na HIV, inda za ta ba da damar yin riga kafi yadda ya kamata. Yana mai cewa, wannan shi ne allurar riga kafin HIV na farko, bayansa ne kuma za'a fara kashi na biyu na gwajin maganin.

Ya zuwa yanzu an dauki sama da masu aikin sa-kai 130, kuma yanzu haka ana gudanar da aikin a wani asibiti a Beijing da kuma wani a birnin Hangzhou.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China