Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta dauki matakai don kara kare 'yancin mallakar fasaha
2019-07-18 19:05:15        cri

A kwanan baya, hukumar kula da ayyukan 'yancin mallakar fasaha ta kasar Sin, ta sanar da wani sabon matakin ikon mallakar ilmin kirkire kirkire da kamfanin sadarwa na Huawei ya samu, wato wata dabarar daukar hoton duniyar wata, da kuma na'urar sadarwar da abun ya shafa. Ban da wannan kuma, a yayin taron zaunannen kwamitin majalisar gudanarwar kasar Sin da aka kira a jiya Labara, an tsai da kudurin daukar jerin matakai, domin kara kare 'yancin mallakar fasaha.

Yanzu Sin na gaggauta aikin kirkire-kirkire, don haka ma ta kara azama ga aikin kare 'yancin mallakar fasaha, wanda ke ba da karfi sosai wajen kirkire-kirkire. Bisa sabbin matakan da Sin ta fitar, za a iya gano cewa, Sin za ta kare 'yancin ne a fannoni hudu.

Na farko dai, za a kare 'yancin bisa doka, a kokarin ba da kariya ga halaltattun muradun kamfanoni, da daidaikun mutane cikin adalci yadda ya kamata. Lamarin da ya nuna cewa, yayin da Sin ke daidaita lamuran da abun ya shafa, to za a bi ma'auni na bai daya domin nuna adalci.

Kana kasar Sin za ta kara mai da hankali kan aikin gyara dokar ikon mallakar fasaha, da dokar ikon rubutun littafi, da dokar lambar shaidar fasaha ta hanyar kara karbar kudin diyya, inda za a tsara tsarin karbar kudin diyya domin horon masu sabawa doka. Misali yayin da ake gudanar da aikin gyara dokar ikon mallakar fasaha a kasar Sin, za a kara karbar kudin diyya har rubi biyar ga masu sabawa doka, adadin kudin da ya kai sahun gaba a fadin duniya. Ban da haka, hukumomin gwamnatin kasar Sin sama da 30, sun riga sun kafa wani tsarin yin horo ga masu sabawa dokar mallakar fasaha cikin hadin gwiwa, inda za su dauki matakai cikin hadin gwiwa, domin sanya takunkumi ko kuma tsorata masu take ikon mallakar fasaha, ta yadda za su kiyaye adalcin zaman takewar al'ummar kasar.

A sa'i daya kuma, domin kaiwa ga ma'aunin kasa da kasa, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata aikin tantance ikon mallakar fasaha, har ma an tabbatar da cewa, kafin karshen shekarar da muke ciki, za a rage wa'adin aikin tantance ikon mallakar fasaha mafi daraja a cikin watanni 17.5, haka kuma za a rage wa'adin yin rajistar lambar shaidar fasaha a cikin watanni biyar, duk wadannan matakai za su sa masu gabatar da roko su samu ikon mallakar fasaha ba tare da bata lokaci ba, tare kuma da kiyaye sakamakon kirkire-kirkirensu a kan lokaci.

Abun mai muhimmanci shi ne, Sin za ta kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasa da kasa, wajen tabbatar da ikon mallakar ilimi don samar da sauki ga kamfanonin kasar wajen tabbatar da hakkinsu a kasashen waje.

A halin yanzu, dan Adam yana cikin lokacin fuskantar sabon babban canji, game da raya kimiyya da fasaha, da yin kwaskwarima kan sana'o'i. Aikin tabbatar da ikon mallakar ilmi shi ne aikin tabbatar da yin kirkire-kirkire. A matsayin kasa dake kan matsayi 20 na gaba mafi yin kirkire-kirkire a shekarar 2018 a duniya, kasar Sin ta kara tabbatar da ikon mallakar ilmi, don biyan bukatunta na sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci, ta hanyar yin kirkire-kirkire, da kuma kara bude kofa ga kasashen waje.

Sin za ta kara yin kirkire-kirkire bisa tushen tabbatar da ikon mallakar ilmi, yayin da take yin kwaskwarima mai zurfi, da kara bude kofa ga kasashen waje, ta hakan za a sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci a kasar a nan gaba. (Masu Fassarawa: Kande, Jamila, Zainab daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China