Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara fadakar da jama'a kan cin abinci dake da amfani ga jikinsu
2019-07-18 14:44:32        cri

Gwamnatin kasar Sin ta bullo da wasu takardu da suka shafi inganta lafiyar al'ummar kasar a kwanakin baya, inda kuma ta dauki wasu muhimman matakan fadakar da jama'a kan riga-kafin kamuwa da cututtuka da yadda za a kula da lafiya baki daya.

Yin kira ga al'umma da su guji cin abinci mai gishiri da mai maiko da mai sukari na daya daga cikin matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka don fadakar da al'umma kan cin abinci dake da amfani ga jikinsu. Babban burin matakan shi ne, nan da shekara ta 2030, yawan gishirin da kowane dan kasar Sin zai ci a kowace rana kada ya wuce giram biyar, kuma yawan man da kowane dan kasar zai ci a kowace rana kada ya wuce giram 25 zuwa 30, sa'annan yawan sukarin da kowane dan kasar zai ci a kowace rana kada ya zarce giram 25.

Kididdiga ta yi nuni da cewa, duba da yadda masana'antu da birane da garuruwa ke kara samun bunkasuwa da kuma saurin karuwar adadin yawan tsoffi, yadda 'yan kasar ke rayuwa gami da aiki ya haifar da wasu cututtukan da ba a san su a baya ba. A halin yanzu, wasu kananan cututtuka na kara yin babbar barazana ga lafiyar Sinawa, ciki har da cutar jijiyoyin zuciya da kwakwalwa, da ciwon daji da cutar da ta shafi lumfashi, da ciwon sukari da sauransu. A nasa bangaren, mataimakin shugaban sashin kula da ingancin abinci na kwamitin kula da kiwon lafiya na kasar Sin Zhang Zhiqiang ya bayyana a kwanakin baya cewa, cin abincin da ba su da amfani ga jikin dan Adam na da babban hadari ga lafiyar al'umma, don haka an yi kira ga al'umma da su guji cin abinci mai gishiri da mai maiko da dauke da sukari fiye da kima. Zhang ya bayyana cewa:

"Ya kamata gwamnati ta tsara tare da aiwatar da wasu ka'idoji, kamar bayanan abubuwan da aka hada abincin ta yadda al'umma za su san abubuwan dake cikin abincin. Haka kuma ya zama dole a yi kokarin kyautata sana'o'in da suka shafi abinci, da kafa dakunan cin abinci masu amfani ga jikin dan Adam da kara gina makarantu masu samar da abinci masu gina jiki. Har wa yau, a shawarci magidanta su guji cin abinci masu gishiri da sukari da maiko fiye da kima, da dafa abinci ta hanyar da ta dace a gida, tare kuma da yin amfani da wasu kayan girki masu amfani ga jikin dan Adam lokacin da ake dafa abinci a gida."

Shi ma a nasa bangaren, shugaban ofishin kula da abinci mai gina jiki da lafiyar dan Adam na cibiyar rigakafi gami da takaita cututtuka ta kasar Sin Ding Gangqiang na ganin cewa, rage yawan gishiri da man girki gami da sukarin da aka sanya a cikin abinci wani muhimmin bangare ne na matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka a wannan karo, inda ya ce:

"Ya kamata a yi kira ga jama'a da su yi amfani da wasu kaya na musamman ta yadda za su rika cin abinci mai gina jiki a gida, ciki har da cokalin auna gishiri na musamman, da butar zuba man girki gami da abun auna kiba. Har wa yau, ya zama dole a rika rubuta muhimman bayanai a kunshin man girki da gishiri da sukari, ta yadda jama'a za su san adadin man girki da gishiri da sukarin da ya kamata su ci a kowace rana. Bugu da kari, ya kamata a baiwa shaguna da kantuna kwarin-gwiwar kafa sashin sayar da abinci maras maiko da gishiri da sukari."

Yayin da gwamnatin kasar Sin ke nuna himma da kwazo wajen fadakar da al'umma kan cin abinci mai gina jiki, tana kuma kokarin samar da abinci mai gina jiki a yankuna masu fama da talauci. Buri na daban da gwamnati ke kokarin cimmawa shi ne, rage saurin karuwar mutane masu kiba. Haka kuma zuwa shekara ta 2022, adadin yara 'yan kasa da shekaru biyar wadanda suka gamu da matsalar rashin girma, ya kamata ya yi kasa da kaso 7 bisa dari, kana kuma zuwa shekara ta 2030, wannan adadi ya kamata ya yi kasa da kaso 5 bisa dari.

Matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka a wannan karo na yin kira ga jama'a da su ci abincin da suke da amfani ga jikin dan Adam sun kara kawar da tunanin gargajiya na al'ummar kasar da dama ta fannin cin abinci. Shugaban ofishin kula da abinci mai gina jiki da lafiyar dan Adam na cibiyar rigakafi gami da takaita cututtuka ta kasar Sin Ding Gangqiang ya yi kira ga al'ummar kasar su tashi tsaye don cin abinci mai gina jiki kuma ta hanyar da ta dace.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China