Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata kasashen yammacin duniya su yi koyi da fasahohin Xinjiang na yaki da ta'addanci
2019-07-16 19:55:13        cri

A 'yan kwanakin baya, zaunannun jakadun kasashen duniya 37 da ke Geneva ciki har da Rasha, Saudiyya, Pakistan da dai sauransu, sun aike da wasika ta hadin gwiwa ga shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, da babbar kwamishiniyar ofishin MDD dake kare hakkin dan Adam, domin nuna goyon bayansu ga dimbin nasarorin da jihar Xinjiang ta kasar Sin ta samu, a fannonin kare hakkin bil Adam, da yaki da ta'addanci, da ma kau da tsattsauran ra'ayi. Lamarin da ya shaida cewa, kasashen duniya na jinjina ga bunkasuwar Xinjiang. Wasu kasashen yammacin duniya da ke yunkurin shafa wa Xinjiang kashin kaji, da ma matsa wa kasar Sin lamba bisa hujjar hakkin dan Adam ba za su ci nasara ba. A maimakon hakan, ya kamata su yi koyi da fasahohin Xinjiang na yaki da ta'addanci, domin warware matsalar da ke addabarsu.

Abin da ya kamata a lura shi ne, a cikin kasashen 37 da suka mika wasikar, akwai wasu kasashe masu bin addinin Musulunci. 'Yan diplomasiyya na wasu kasashe sun taba ziyartar Xinjiang a watan Yunin bana, wadanda suka gane wa idanunsu yadda ake samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, da jituwar zamantakewar al'umma a yankin. Don haka kalamansu kan batun Xinjiang na da karfi. Lamarin da ya sa ake ganin cewa, zargin da wasu kasashen Turai 22 suka yi wa manufofin addini, da hakkin bil Adam a kwanakin baya ba shi da tushe ko kadan.

A hakika dai, wadannan kasashe sun dauki ma'auni biyu a kan batun yaki da ta'addanci, nufinsu shi ne tsoma baki kan harkokin cikin gidan Sin ta hanyar amfani da batun Xinjiang.

Alal hakika, kasashen yammacin duniya sun nuna sha'awa kan batun jihar Xinjiang ta kasar Sin, musamman ma a cikin 'yan watannin da suka gabata. Wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasashen, suna dinga yada jita-jitar dake da nasaba da batun, suna cewa wai cibiyar horaswa ta kwarewar sana'o'i da aka kafa domin sauya halayyar masu tsattsauran ra'ayi a Xinjiang, sansani ne na horon masu laifi. Har ma sun zargi matakan yaki da ta'addanci, da sauya halayyar masu tsattsauran ra'ayi da gwamnatin kasar Sin ta dauka bisa doka, kamar yadda suke so.

Tun daga shekarun 1990 na karnin da ya gabata, kungiyar 'yan ta'adda, da kungiyar 'yan kawo baraka ga kasa, da kungiyar masu tsattsauren ra'ayin addini, sun rika aikata ayyukan ta'addanci daya bayan daya, hare-haren ba ma kawai sun sa fararen hula da ba su ci ba su sha su rasa rayuka ko jin rauni, har ma sun kawo illa ga ci gaban tattalin arzikin yankin. Domin dakile matsalar, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai a jere bisa doka.

Kafa cibiyar horaswar kwarewar sana'o'i, daya ne dake cikin matakan, inda ake samar da horaswar sana'o'i kyauta ga masu tsatsauren ra'ayi, domin sauya halayyarsu ta hanyar koyon yaren Han, da ilmomin doka, da kwarewar sana'o'i. Makasudin kafuwar cibiyar shi ne kawar da ta'addanci daga tushensa ta hanyar sauya halayyar masu tsatsauran ra'ayi, tare kuma da samar musu guraben aikin yi.

An shaida cewa, an samu nasarori wajen magance ta'addanci ta hanyar kafa cibiyar ba da ilmi. Ya zuwa yanzu, ba a samu lamarin ta'addanci a kimanin shekaru uku da suka gabata ba a yankin Xinjiang. Yawan GDP na yankin Xinjiang na shekarar 2018 ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na shekarar 2017, kana yawan masu yawon shakatawa da suka zo yankin a dukkan shekarar ya kai miliyan 150, wanda ya karu da kashi 40 cikin dari. A matsayin yanki mafi bude kofa ga kasashen waje dake yammacin kasar Sin, yankin Xinjiang yana yin amfani da shawarar "ziri daya da hanya daya", wajen kara samun damar ci gaba.

Ta'addanci da tsattauran ra'ayi su ne kalubalen da dukkan duniya ke fuskanta tare, ciki har da kasashen yammacin duniya. Idan aka dauki ma'auni biyu wajen yaki da ta'addanci, za a kawo illa kan masu daukar matakan. Jama'ar yankin Xinjiang suna da ikon yin magana game da yanayin Xinjiang, kuma kasashen yammacin duniya ba su da iznin tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin ta wannan batu. Ya kamata wasu kasashen yammacin duniya su tura wakilai zuwa yankin Xinjiang, su ganewa idanun su tare da koyon fasahohin yaki da ta'addanci, don taimakawa warware matsalolinsu na yaki da ta'addanci. (Masu Fassarawa: Kande, Jamila, Zainab daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China