Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta karfafa aikin kula da lafiya kwakwalwa
2019-07-16 11:07:51        cri

Gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakan kula da lafiya mutane masu fama da lalurar tabin hankali, a yayin da kasar ta sha alwashin inganta lafiyar kashi 80 bisa 100 na mutane masu fama da cutar damuwa, nan da shekarar 2030, a wata sanarwa da mahukuntan kasar suka bayyana a jiya Litinin.

Shirin lafiyar na Healthy China Action (2019-2030), an tsara shi ne karkashin wani kwamitin musamman wanda majalisar gudanarwar kasar Sin ta kafa a kwanan nan.

Kasar Sin tana samun yawaitar karuwar mutane masu fama da cutar tabin hankali da matsalolin sauyin halayya, kuma mafi yawan jama'a suna da karancin ilmi game da irin wadannan matsaloli, sakamakon karancin wayar da kan jama'a game da yadda za su yi rigakafin matsalolin har ma da yadda za su iya tunkarar matsalolin idan sun faru, in ji sanarwar.

Matakan da hukumomin suka kuduri aniyar aiwatarwa, sun hada da karfafa ilmin lafiyar kwakwalwa ta hanyoyi daban daban, kakkafa wasu dakunan duba lafiyar kwakwalwa a wuraren zaman jama'a, da kuma daga matsayin kwararru ta hanyar samar da manyan kwalejojin nazarin matsalolin da suka shafi tunanin bil adama. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China