Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Sin yana tafiya yadda ya kamata
2019-07-15 19:58:56        cri

Alkaluman kididdigar da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a yau Litinin, sun nuna cewa, a cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP na kasar Sin, ya kai Yuan kimanin tiriliyan 45.09, wanda ya karu da kashi 6.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Bisa yanayin fuskantar ra'ayin bangare daya, da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da tattalin arzikin duniya ke ciki, abu ne mai wuya, a kiyaye tafiyar tattalin arzikin Sin yadda ya kamata, don haka ana iya cewa, sakamakon da aka samu ya nuna bunkasuwar tattalin arziki bisa yanayi da ake ciki.

Tun daga shekarar bara, an fuskanci yanayin rashin tabbas a kasashen waje, kuma Sin ta fuskanci matsin lamba kan raguwar tattalin arzikinta. Kaza lika saurin bunkasuwar tattalin arzikinta ya karu da kashi 6.3 cikin dari, wanda ya yi kasa kadan, idan aka kwatanta shi da na watanni 3 na farkon bana, wato kashi 6.4 cikin dari, amma an samu wannan karuwa ne bisa yanayin raguwar tattalin arzikin duniya, kana yana cikin ma'aunin da gwamnatin kasar Sin ta tsara a tsawon shekara, wato daga kashi 6 zuwa 6.5 cikin dari, wanda ya dace da hasashen da aka yi, na canja tsarin bunkasa tattalin arzikin Sin daga yanayin sauri zuwa mai inganci.

Ko da yake har yanzu dimbin kasashe ba su sanar da alkaluman tattalin arzikinsu ba, amma bisa hasashen da kungiyar kasa da kasa mai ruwa da tsaki ta yi, an ce, wannan saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin na farkon rabin shekarar bana wato kaso 6.3 bisa dari, yana kan gaba a cikin manyan kasashe, da yankuna masu saurin ci gaban tattalin arziki a duk duniya. A halin yanzu dai, yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar ga duniya ta fuskar karuwar tattalin arziki, ya kai kashi 30 cikin dari. A nan gaba ma, Sin za ta ci gaba da kasancewa tamkar muhimmin injin sa kaimi ga karuwar tattalin arzikin duniya.

A wannan yanayi mai sarkakiya da duniya ke ciki a yanzu, tattalin arzikin Sin na kara samun bunkasuwa mai inganci, lamarin da ba a iya raba shi da kokarin gwamnatin Sin, da ma kamfanoninta. Ganin yadda gwamnatin Sin ke tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da manufofin kudi cikin yakini yadda ya kamata, har ma ta dauki matakin rage yawan harajin da aka buga wa kamfanoninta, har Yuan triliyan 2 domin tabbatar da gudanar da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

A sa'i daya, gyaran fuskan da ake yi wa kamfanoni mallakar gwamnatin kasar, domin su shiga kasuwa yadda ya kamata ya samu babban ci gaba, haka kuma ana kokarin hada kamfanonin domin su kasance cikin babban rukuni, kana kamfanoni masu zaman kansu, suna kara shiga sabbin sassan tattalin arzikin kasar da ba su taba shiga a baya ba. Ban da haka, an samu sakamako mai faranta rai a fannin kyautata sana'o'in gargajiya, ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohi. Kaza lika kamfanonin jarin waje sun nuna yabonsu kan matakan da kasar Sin ta dauka a bangaren bude kofa ga kasashen waje, har ma sun tsaida kudurin kara zuba jari a kasar. A don haka adadin jarin wajen da aka zuba a kasar Sin a cikin watanni shida na farkon shekarar bana, ya karu bisa kaso 7.2 cikin dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara. Duk wadannan sun nuna cewa, zamantakewar al'ummar kasashen duniya, suna cike da imani kan tattalin arzikin kasar Sin.

Bana ake cika shekru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, ita ce kuma shekara mafi muhimmanci da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta tabbatar da kafa zaman al'umma mai matsakaicin karfi daga duk fannoni a kasar ta Sin. Duk da cewa, tattalin arzikin duniya ya gamu da wahala, amma tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da samun bunkasuwa kamar yadda ake fata. Ko shakka babu, gwamnatin kasar Sin ta yi kokari matuka, lamarin da ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfi, har yana iya dakile kalubalen da yake fuskanta. Shi ya sa tattalin arzikin kasar Sin ke samun ci gaba mai inganci cikin lumana, kuma ya dace kasashen duniya su nuna imani ga makomar tattalin arzikin kasar ta Sin. (Masu Fassarawa: Zainab, kande, Jamila daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China