Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin da hukumar FAO sun hada hannu wajen inganta sana'ar noma a yankunan karkara
2019-07-13 16:15:03        cri
Kasar Sin da hukumar kula da aikin gona da samar da abinci ta MDD FAO, sun hada hannu wajen inganta sana'ar noma a yankunan karkara masu fama da talauci na kasar.

Shirin mai taken "Raya Muradun Ci Gaba Masu Dorewa a Kauyuka", zai gudana ne tsakanin shekarar 2019 da 2021 a kauyuka 16 masu fama da talauci.

A karkashinsa, za'a horar da jama'ar kauyukan kan dabarun noma ba tare da amfani da sinadarai ba da yadda za su sayar da amfanin gonarsu ta dandalin intanet da kuma inganta yadda suke kunshe su da sauran wasu bangarori.

Ana sa ran sama da manoma 1,000 ne za su amfana kai tsaye daga shirin, wanda aka zubawa jarin dala miliyan 1.

Har ila yau, shirin na da burin aiwatar da manufar farfado da yankunan karkara ta kasar Sin da kuma cimma muradun ci gaba masu dorewa, da samar da dabarun yaki da talauci da za'a iya koyar da sauran kasashe masu tasowa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China