Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikin waje da kasar Sin ke yi yana da karfi sosai
2019-07-12 21:00:16        cri

A yau Juma'a, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da alkaluman shige da fice da kasar Sin ta samu a watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, inda alkaluman suka kai kudin Sin RMB yuan triliyan 14.67, wato ya karu da kashi 3.9 cikin dari bisa makamancin lokacin bara. Ba abu ne mai sauki ba na yadda kasar Sin ta samu wannan kyakkyawan sakamako a lokacin da matakan kare cinikin waje suke tsananta, kuma yawan cinikin waje da ake yi a duk fadin duniya yake raguwa. Wadannan alkaluma sun kuma bayyana cewa, cinikin waje da kasar Sin take yi yana da karfi sosai. Har yanzu, tattalin arzikin kasar Sin zai dade yana kara samun ci gaba mai dorewa kamar yadda ake fata, wannan yanayi bai canja ba.

Idan aka nazarci alkaluman, za a ga cewa, a fannoni 3 ne cinikin waje na kasar Sin yake bayyana yadda yake samun ci gaba mai dorewa kuma mai inganci.

Da farko dai, dalilin da yake sa kasar Sin ta kara samun karuwar cinikin waje, saboda yana da karfi sosai. A cikin watanni shida na farkon shekarar bana, yawan kayayyaki masu dauke da fahohin zamani da kasar Sin ta fitar da su zuwa ketare ya karu da kaso 5.5% bisa makamancin lokacin bara, kuma ya kai kusan 60% bisa na jimlar kayayyakin da kasar Sin ta fitar da su. Sannan yawan kayayyakin da kamfanoni masu zaman kansu suka samar kuma suka fitar ya karu da 11% bisa makamancin lokacin bara. Sakamakon haka, yanzu, kamfanoni masu zaman kansu sun zama muhimmin karfi ga cinikin waje da kasar Sin take yi. Wadannan alkaluma sun bayyana cewa, kasar Sin na samun sabon ci gaba wajen inganta tattalin arzikinta.

Na biyu, an kara samun abokan cinikayya. A cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, ko da yake yawan kayayyakin da aka yi shigi da fici a tsakanin Sin da Amurka ya ragu da kashi 9 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, amma yawan kayayyakin a tsakanin Sin da wasu muhimman abokan cinikayya, ciki har da EU, ASEAN da kuma kasar Japan da dai sauransu ya karu da kashi 11.2 cikin dari, da 10.5 cikin dari, da kuma 1.7 cikin dari bi da bi. Musamman ma a tsakanin kasashen dake da nasaba da shawarar "Ziri daya da hanya daya", adadin ya karu da kashi 9.7 cikin dari. Ban da wannan kuma, karuwar cinikayya a tsakanin Sin da wasu kasuwanni masu tasowa, ciki har da yankin Latin Amurka, da nahiyar Afirka da dai sauransu ta kai kashi 7.4 cikin dari da kashi 9 cikin dari. Wannan ya nuna cewa, an soma samun riba sakamakon matakin da kasar Sin ta dauka kan kyautata tsarin kasuwar duniya, wanda zai amfanawa kasar Sin wajen kawar da mummunan tasirin da takaddamar cinikayya a tsakanin ta da kasar Amurka, tare kuma da kara karfin kasar Sin na tinkarar hadurra.

Na uku, an kara kyautata tsarin kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa ketare. A cikin watanni shida na farkon bana, kasar Sin ta kara fitar da kayayyakin da suka shafi injuna da na lantarki da wadanda ake bukatar ma'aikata da yawa wajen kera su. Wannan ya nuna cewa, kayayyakin da kasar Sin ta fitar na kara samun karfin takara.

Abun lura a nan shi ne, bisa yanayin da ake ciki na karuwar takaddamar cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Amurka da kasar Amurka ta tayar, rarar kudin da kasar Sin ta samu kan cinikayya a tsakaninta da Amurka ta karu da kashi 12 cikin dari, wannan ya nuna cewa, kara sanya harajin kwastam bai warware matsalar rashin daidaito a tsakanin kasashen biyu ba, a maimakon haka ma sai dai ya lalata moriyar kamfanoni da masu sayayya na kasar Amurka.

Duba da yanayin cinikayya ya tabarbare a duk fadin duniya, kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ta rage hasashen da ta yi kan karuwar kasuwancin duniya daga kaso 3.7 zuwa 2.6 bisa dari a watan Afrilun bana. Amma duk da haka, cinikin waje da kasar Sin ta yi ya bunkasa yadda ya kamata a watanni shida na farkon bana, al'amarin da ya shaida cewa, kasar Sin na da babbar kasuwa da dimbin al'umma gami da cikakken tsarin masana'antu, wadanda suka taimaka sosai ga bunkasuwar kasuwancin waje.

Har wa yau, kasar Sin na ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje da rage harajin kwastam, matakan da suka karfafa gwiwar kasuwanni gami da kamfanoni. A yayin taron majalisar gudanarwar da aka yi a kwanakin baya, Sin ta tsara wasu muhimman manufofi na saukaka matakan yin kasuwanci da kyautata yanayin kasuwanci tare kuma da sanya sabon kuzari ga harkokin kasuwancin kasar Sin, ciki har da nazarin ci gaba da rage biyan harajin kwastam kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar, da gaggauta raya harkokin kasuwanci ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa, da raya yankunan cinikin shigowa da kayayyaki daga kasashen waje na gwaji da rage lokacin da ake batawa don shigo da kayayyaki daga kasashen waje. (Sanusi Chen, Bilkisu Xin, Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China