Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Baki Sun Kara Amincewa Da Yanayin Tattalin Arzikin Kasar Sin
2019-07-11 20:48:08        cri
Alkaluman kididdiga da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar a yau Alhamis na nuna cewa, yawan jarin waje da aka zuba a cikin kasar a watanni shida na farkon wannan shekara ya kai biliyan 47.833, adadin ya karu da kashi 7.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Duk da hadurran da tattalin arziki da duniya ke fuskanta da raguwar saurin karuwar yawan jarin da baki suke zubawa kai tsaye a fadin duniya (FDI), yawan jarin waje da ake zubawa a kasar Sin yana ci gaba da karuwa, a hakika wannan ya nuna cewa, baki sun kara amincewa da tattalin arzikin kasar ta Sin.

Kididdigar ta kuma nuna cewa, akwai wasu muhimman abubuwa guda biyu game da yanayin jarin waje da baki suka zuba a kasar Sin. Da farko, an soma zuba jari a matsayin kasa-kasa kan sana'o'in harhada da kara gyara kayayyaki zuwa matsayin matsakaici da babban matsayi, yawan jarin waje da aka zuba a fannin sana'o'in kimiyya da fasaha na zamani na kasar Sin ya karu da kashi 44.3 cikin dari, wato ya kai kashi 28.8 bisa na dukkan jarin waje da aka zuba a kasar. Irin wannan sauyi ya dace da yanayin da ake ciki na kyautata tsarin tattalin arzikin kasar Sin daga samun ci gaba cikin sauri zuwa samun ci gaba mai inganci. Na biyu, yadda manyan yankuna da kungiyoyi da suka zuba jari a kasar, na tafiya yadda ya kamata, ciki har da karuwar yawan jarin waje da kasashen Koriya ta kudu, Japan, Jamus da kungiyar Turai suka zuba a cikin kasar ta Sin wadanda suka kai kaso 63.8, kaso 13.1, karo 81.3 da kuma kaso 22.5 bi da bi. Dukkansu sun nuna cewa, har yanzu kasar Sin ta kasance muhimmin yanki da baki suka fi son zuba jari.

Ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci da na nuna bangaranci na dada yaduwa a duk fadin duniya, kuma 'yan kasuwan kasa da kasa ba su da kwarin-gwiwar zuba jari. Amma a watanni shida na farkon shekarar bana, adadin yawan jarin wajen da kasar Sin ta jawo ya karu, al'amarin da ya sake nuna sirrin tattalin arzikin kasar Sin na jawo hankalin masu zuba jari.

Kasar Sin na da dimbin al'umma da yawansu ya kai biliyan 1.4 gami da masu matsakaitan kudin shiga da dama, wadanda suka samar da babbar riba ga 'yan kasuwan waje da suka zuba jari a kasar Sin. A shekara ta 2018, a bangaren manyan masana'antu, jimillar ribar da kamfanonin da baki 'yan kasuwa gami da 'yan kasuwan Hong Kong da Macau da Taiwan suka zuba jari a ciki suka samu ta zarce Yuan triliyan 1.6, wadda ta karu da kaso 1.9 bisa dari.

Duk da cewa, tattalin arzikin duniya na fuskantar tawaya a halin yanzu, amma kasar Sin na kara fadada bude kofarta ga kasashen waje da kyautata yanayin gudanar da kasuwanci, abun da ya kwantar da hankalin kamfanonin kasashen waje dake Sin. Gwamnatin kasar Sin tana nuna himma da kwazo wajen karfafa gwiwar baki 'yan kasuwa don su zuba jari a kasar, ciki har da kara rage musu harajin kwastam, da habaka sana'o'i da bangarorin da baki 'yan kasuwa za su iya zuba jari a ciki, da amincewa da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa don nuna adalci ga masu jarin gida da na waje, tare kuma da sanar da wasu muhimman matakai biyar na gaggauta bude kofa ga kasashen ketare a yayin taron kolin kasashen G20 da aka yi a birnin Osakar kasar Japan.

Ko da yake ana fama da matsalar ba da kariyar ciniki a duk fadin duniya, amma a maimakon janye jari daga kasar Sin, kasashen waje na ci gaba da kara zuba jari a kasar. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da tattalin arzikin Sin da ke samun kyautatuwa wata kyakkyawar dama ce a gare su. Babu shakka dukkan kamfanonin jarin waje da ke son samun ci gaba tare da tattalin arzikin Sin za su kara samun alfanu daga yadda Sin ke karfafa yin kwaskwarima a gida da bude kofarta ga waje.(Masu Fassara: Bilkisu, Murtala, Kande, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China