Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka za su samu kyakkyawar makoma a nan gaba muddin sun habaka hadin gwiwarsu bisa ka'idar samun moriyar juna
2019-07-11 13:50:38        cri

An gudanar da taron kara wa juna sani kan halin da kasashen Sin da Amurka suke ciki ta fuskokin tattalin arziki da ciniki, da kuma makomar da za su samu a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, daga ranar 9 zuwa 10 ga watan.

Yayin da babban jami'in CEO na hadaddiyar kungiyar kasuwanci ta jihar Texas ta kasar Amurka Jeff Moseley, ya zanta da wakilinmu, ya yi nuni da cewa, Sin da Amurka, sun aza harsashi mai kyau ta fuskar yin hadin gwiwar ciniki. Shugabannin kasashen 2 sun cimma daidaito mai muhimmanci a yayin taron kolin Osaka na G20. Har ila yau Sin da Amurka, za su samu kyakkyawar makoma a nan gaba, muddin sun habaka hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da ciniki, bisa ka'idar samun moriyar juna.

Mista Jeff Moseley ya yi bayani cewa, tun bayan da kasashen Sin da Amurka suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu a shekarar 1979 har zuwa yanzu, hadin gwiwar da ke tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki ta kawo alheri ga jama'arsu duka. Kasashen 2 sun aza harsashi mai kyau wajen yin hadin gwiwa ta fannin ciniki. "Yau shekaru 40 ke nan da Sin da Amurka suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu. Ko shakka babu huldar da ke tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki ta amfana musu sosai, wannan shi ne ainihin dalilin da ya sa aka yi ciniki. Yayin da suke raya huldarsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki yadda ya kamata, sai za su ci gajiya duka, alkaluman kididdiga su ma sun iya faranta rayukan mutane. Kana kuma, masu sayayya na Amurka sun ci gajiya sosai daga irin wannan kyakkyawar hulda. Har ila yau mutane da yawa sun yi amfani da damamaki daga bunkasuwar kasar Sin. Muna farin ciki da ganin, Sin da Amurka sun aza harsashi mai kyau ta fuskar yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki."

Mista Moseley ya nuna cewa, shugabannin kasashen 2 sun cimma daidaito mai muhimmanci a yayin taron kolin Osakan Japan, inda suka amince da maido da tattaunawa ta fuskar tattalin arziki da ciniki, lamarin da ya faranta rayukan mutane sosai. Shi ma ya sa ran samun nasara a yayin tattaunawa ta sabon zagaye. "Shawarwarin da shugabannin kasashenmu 2 suka yi a Osaka ya faranta mana rai sosai. Kafin taron kolin Osakan, Sin da Amurka sun kasance cikin zaman dar-dar. Ina farin ciki da ganin shugabanninmu 2 sun zauna tare, sun yi shawarwari yadda ya kamata, inda suka yarda da maido da tattaunawar tattalin arziki da ciniki a nan gaba. Jiharmu ta Texas mun yi imani da cewa, za a samu nasara a tattaunawar da Sin da Amurka za su maido da ita a nan gaba."

Mista Moseley ya yi karin bayani da cewa, jihar Texas, jiha ce wadda ta fi sayar da kayayyaki zuwa kasashen ketare a Amurka baki daya. Kasar Sin, abokiyar ciniki ce ta uku gare ta. Yana sa ran cewa, jiharsa za ta kara hadin kai da kasar Sin ta fuskar iskar gas da danyen mai da dai sauransu. Haka zalika kuma, mista Moseley ya ce, hadaddiyar kungiyar kasuwanci ta jihar Texas tana da dogon tarihi na shekaru kusan dari daya, wadda take himmantuwa wajen kara azama kan ci gaban tattalin arziki da ciniki. A cewar mista Moseley, yin ciniki da kasar Sin yana da nasaba da samun aikin yi a wurin. "Yau shekaru 20 da suka wuce, jiharmu ta kafa huldar ciniki da Sin. Yanzu muna shirya kafa wani kawance. Yin ciniki da kasar Sin yana da nasaba da samun aikin yi a jiharmu."

A yayin da aka kusan kammala zantawar, mista Moseley ya yi kira ga shugabannin kasashen Amurka da Sin da su aiwatar da ra'ayi daya da suka cimma a yayin shawarwarinsu a taron kolin Osakan, a kokarin cimma yarjejeniyar samun moriyar juna. Ya kuma yi nuni da cewa, Sin da Amurka za su samu kyakkyawar makoma a nan gaba muddin su habaka hadin gwiwarsu bisa ka'idar samun moriyar juna. "Muna bukatar cimma wata yarjejeniyar samun nasara tare, a kokarin tabbatar da samun moriyar juna a tsakanin Sin da Amurka. Wannan yana da muhimmanci sosai. Muddin mun daidaita wasu batutuwan da muka sa kulawa a kai, sai za mu iya gano wasu fannonin samun moriyar juna, ta haka za mu samu kyakkyawar makoma." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China