Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka na yunkurin dakile kasar Sin bisa maganar Taiwan a wani mataki ne mai hadari
2019-07-10 14:17:30        cri

Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta matuka, game da iznin da majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta bayar, na sayawar yankin Taiwan makamai da darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 2.22.

Matakin da Amurka ta dauka a wannan karo, ya sabawa ka'idar kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyin hadin gwiwa guda uku tsakanin kasashen biyu, kuma ya keta matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ganawar tasu ba da dadewa ba a birnin Osaka. Kana matakin tsoma baki ne kan harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma mataki ne mai hadari sosai a cikinsa.

A shekarun baya-baya nan, Amurka ta kan daidaita alakar yankin Taiwan da babban yankin kasar Sin bisa tsarin "Sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da doka guda daya". Sanarwoyin hadin gwiwa guda uku na nufin sanarwa irin wannan tsakanin Sin da Amurka, wadanda suka tabbatar da ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, wato Amurka ta mai da gwamnatin jamhuriyyar jama'ar kasar Sin halaltaciyar gwamnati daya tilo a kasar Sin, kuma Taiwan ya kasance wani yanki ne na kasar Sin. Daga cikinsu kuma, sanarwar hadin gwiwa da suka kulla a ran 17 ga watan Agustan shekarar 1982 ta kayyade cewa, kamata ya yi Amurka ta takaita yawan makamai da za ta sayarwa Taiwan, ta yadda za ta kai ga daina sayarwa yankin makamai. Amma, Amurka ta ci gaba da taimakawa yankin Taiwan ta fuskar makamai bisa dokar dangantakar Taiwan da ta fitar.

Matakin dai ya kawo babbar illa ga dangantakar Amurka da Sin. Gwamnatin Amurka mai ci ta sayarwa yankin Taiwan makamai har sau hudu, tun lokacin da ta hau kan mukaminsu yau shekaru biyu da suka gabata da wani abu. Ba ma kawai lamarin ya biya bukatun masu sayar da makamai na cikin Amurka ba, har ma ya nuna yadda Amurka take yunkurin matsa lamba da kuma haddasa cikas ga kasar Sin.

Amurka na yunkurin sayarwa yankin Taiwan makamai yadda take so a kullum ta hanyar zartas da wasu dokoki, ciki hadda majalisar wakilai da ta dattawa, sun zartas da "dokar yawon shakawata a Taiwan", wadda ta baiwa dukkanin jami'an kasar iznin kai ziyara yankin Taiwan, kuma majalisar wakilai ta zartas da "dokar ba da tabbaci ga Taiwan na shekarar 2019".

Duk wadannan matakan da Amurka ke dauka na bayyana tsoron wasu 'yan siyasar Amurka, saboda ganin saurin bunkasuwar kasar Sin a shekarun baya bayan nan. Amurka tana amfani da yankin Taiwan don haddasa cikas ga kasar Sin, a halin da ake ciki na rashin samun daidaituwar dangantaka a tsakanin Sin da Amurka, tana kuma da mummunan nufi na kara matsawa kasar Sin lamba.

Yunkurin wasu 'yan siyasar Amurka na yin amfani da yankin Taiwan don kawo cikas ga kasar Sin ba zai cimma nasara ba ko kadan. A hannu guda, duk da cewa wasu 'yan siyasar yankin Taiwan, wadanda suke mantawa da tarihinsu, na yunkurin yin jayayya da babban yankin bisa goyon bayan Amurka, amma ba za su iya hana tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya da zukatan jama'a ba. Ya zuwa yanzu, bangarorin biyu na kafa tsare-tsaren hadin kai, wadanda ba za su iya yin ban kwana da juna ba a fannin masana'antu da samar da kayayyaki. Babban yankin ya kasance aminiyar ciniki mafiya girma ga Taiwan, da kasuwa mafiya girma ga Taiwan, inda yake shigar mata da kayayyaki, kana wuri mafi muhimmanci da yake zubawa jari.

Wasu alkaluma sun bayyana cewa, yawan kudin dake shafar cinikayyar da aka yi tsakanin yankin Taiwan da babban yankin kasar Sin a shekarar 2018, ya zarce dalar Amurka biliyan 200. Kana yawan mazauna Taiwan da suka bude ido a babban yankin ya kai fiye da miliyan 4. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu na kokarin kara tuntubar juna a dukkanin fannoni, abin da zai haifar da cin gajiyar jama'ar bangarorin biyu. Saboda ganin hakan, kafofin yada labarai na Taiwan na nuna cewa, Amurka na fatan ganin dangantakar dake tsakanin bangorin biyu ta kara tsananta, ta yadda hakan za ta iya sayarwa yankin Taiwan karin makamai. Amma fa babu yiwuwar samun karin bunkasuwa mai dorewa idan yankin ya dogaro da taimakon Amurka.

Babban yankin na kokarin gudanar da tsarin yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga ketare a cikin shekaru 40 da suka gabata, don cimma muradunsa na farfado da al'ummar Sinawa, kuma yanzu ya kusan cimma hakan, matakin da ya bayyana tushe, da kuma sharadi mafi kyau wajen dunkulewar bangarorin biyu waje guda.

Saboda ganin haka, kafofin yada labarai na yankin Taiwan na ganin cewa, babban yanki na rike da ragamar bunkasuwar dangantakar bangarorin biyu. A hannu guda kuma, wasu kasashe sun katse huldar diplomasiyya da yankin Taiwan, da kafa ko farfado da hulda irin wannan da babban yanki, matakin da ya bayyana cewa, manufar kasar Sin daya tak a duniya, sanin kowa ne. Gudanar da harkoki na kashin kansa ya mayar da Taiwan saniyar wane ke nan. Dukkanin wadannan abubuwa sun bayyana cewa, tilas ne Sin ta dunkule, ba kuma wanda zai hana ta hakan.

A yayin ganawar shugabannin Sin da Amurka a Osaka kwanan baya, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da raya dangantakarsu bisa tushen yin sulhu, da hadin kai, da samar da daidaito. Kuma suna cimma matsaya daya kan farfado da sulhuntawa ta fuskar cinikayya, bisa tushen adalci da mutunta juna. A daidai wannan lokaci kuma, Amurka ta yanke shawarar sayarwa yankin Taiwan makamai, abun da ya yi kunnen uwar shegu da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimmawa, wanda kuma zai kawo illa ga dangantaka, da kuma zaman lafiya da karko tsakanin babban yanki da yankin Taiwan, kuma zai kawo cikas ga kokarin da Sin da Amurka suke yi na daidaita bambancin ra'ayinsu.

Makaman da Amurka za ta sayarwa yankin Taiwan ba za su ba shi cikakken tsaro ba ko kadan, hanya daya tilo da yankin zai bi ita ce dunkulewar kasar Sin daya tak, kuma jama'ar yankin za su ci gajiyar muradun farfado da al'ummar Sinawa baki daya. Kasar Sin na da niyya da kuma cikakken imanin kiyaye ikon mulkin kasa, da cikakkun yankinsa, da kuma kiyaye zaman lafiya da karko tsakanin babban yankin da Taiwan, wanda ba wata kasa ta daban za ta iya hana hakan.

Hakikanin halin da ake ciki yanzu na shaida cewa, halin da bangarorin biyu ke ciki, kuma dangantakar dake tsakaninsu na samun bunkasuwa yadda ya kamata, ba wanda zai hana wannan ci gaba. Ko shakka babu, kasar Sin za ta ci gaba da bunkasuwa, da farfado da al'ummarta, da dunkulewar bangarorin babban yanki da yankin Taiwan waje guda. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China