Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron kasa da kasa game da hadin gwiwar raya ilmi, da musaya tsakanin masanan Sin da na Tarayyar Najeriya
2019-07-11 08:57:19        cri

A ranar Laraba 26 ga watan Yuni ne aka bude taron kasa da kasa, game da hadin gwiwar raya ilimi, da musaya tsakanin masanan Sin da na tarayyar Najeriya, a jami'ar Zhejiang normal ta horas da malamai, dake birnin Jinhua a lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin.

A dai wannan rana, an kaddamar da cibiyar bincike game da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin raya Ilimi. Kana an gabatar da rahoton shekara game da musaya, tsakanin masanan Sin da na Afirka ta kudu.

Har ila yau, an sanya hannu kan takardar fahimtar juna ta kulla hadin gwiwa tsakanin jami'ar Zhejiang normal, da jami'ar Modibbo Adama ta Yolan jihar Adamawa, da kuma jami'ar Ibadan duka daga tarayyar Najeriya.

Masana da jagororin wasu hukumomin Sin da na jami'oin Najeriya ne suka halarci wannan taro, ciki kuwa hadda farfesa Wang Heng, sakataren jami'iyyar kwaminis reshen jami'ar, kuma mataimakin darakta a cibiyar nazarin harkokin Afirka a jami'ar Zhejiang normal, da darakta a ofishin tsara samar da ci gaba, da asusun yaki da fatara a nahiyar Afirka Mr. Wu Peng, da mataimakin darakta a cibiyar bincike da musaya tsakanin masanan Sin da nahiyar Afirka Yang Hui.

Daga Najeriya kuwa, taron ya samu halartar mataimakin shugaban Jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya dake Jos farfesa Seddi Sebastian Maimako, da mataimakin shugaban Jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Ibadan farfesa Adebola Babatunde Ekanola, da takwaransa na jami'ar Modibbo Adama dake birnin Yolan jihar Adamawa farfesa Usman Abdullahi wurochekke, da kuma mukaddashin mataimakin shugaban Jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya Benin Micheal Emefiele Aziken da dai sauran su.

Mahalartan sun gabatar da makaloli da dama, wadanda suka kunshi irin kalubale dake tattare da burin da ake da shi, na inganta samar da ilimi a manyan makarantun Najeriya, da irin rawar da hadin gwiwar jami'oin Sin da na Najeriya zai taka, wajen cimma moriyar juna tsakanin sassan biyu.

A jawabin sa na godiya a madadin tawagar bakin da suka halarci wannan taro daga Najeriya, mukaddashin mataimakin shugaban Jami'ar gwamnatin tarayyar Najeriya Benin Micheal Emefiele Aziken, ya godewa mashirya taron, da jami'ar Zhejiang normal, wadda ta samar da cibiyar bincike domin raya ilimi da inganta musaya tsakanin masanan Sin da na tarayyar Najeriya. Ya kuma yi fatan dorewar hadin gwiwar sassan biyu, da kuma fatan cimma nasarar aiwatar da kudurorin dake kunshe cikin hadin gwiwar sassan. (Saminu, Ibrahim / Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China