Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang ta kara bude kofa ga kasashen waje
2019-07-05 13:40:00        cri

Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, tana tsakiyar yankin nahiyar Asiya da Turai, da kuma arewa maso yammacin kasar Sin. Kana tana makwabtaka da kasashe takwas da suka hada da Mongoliya, da Rasha, da Kazakhstan, da Kyrghyzstan, da Tajikistan, da Afghanistan, da Pakistan, da Indiya da sauransu, kuma tsawon iyakar jihar da kasashen ya kai fiye da kilomita 5700, ita ce jiha mafi fadi a kasar Sin, haka kuma jiha ce da ta fi tsawon iyaka da kasashen da suke makwabtaka da ita a kasar Sin.

A shekarun baya baya nan, a sakamakon raya shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, jihar Xinjiang ta yi kokarin kara bude kofarta ga kasashen waje.

A bangaren gina hanyoyin motoci, a halin yanzu jihar Xinjiang ta bude hanyoyin motoci 111 a tsakaninta da kasashe 5. Kana a bangaren gina hanyoyin jiragen kasa kuwa, an hade birnin Urumqi, babban birnin jihar, da sauran sassan kasar da hanyoyin jiragen kasa mai saurin tafiya. Har wa yau, daga shekarar 2014 har zuwa yanzu, an gina sabbin hanyoyin jiragen kasa a jihar Xinjiang da suka kai tsawon kilomita 1320, abin da ya sa gaba dayan tsawon hanyoyin jiragen kasa a jihar kai tsawon kilomita 6231.

A fannin jiragen sama, yawan filayen jiragen sama na amfanin al'umma a jihar ya kai 21. Ya zuwa karshen watan Mayu na shekarar 2019, yawan hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama a jihar ya kai 264, akwai kuma zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin birnin Urumqi da birane fiye da 80 na kasar ta Sin da kuma birane fiye da 20 na kasashen waje.

A fannin harkokin sadarwa kuwa, an bude hanyoyin sadarwa 17 a tsakanin jihar da sauran kasashen dake makwabtaka da ita, hakan ya hada jihar Xinjiang da kasashen a fannin harkokin sadarwa, kuma an kafa zirin tattalin arziki na hanyar siliki a tsakaninta da sassan da suke makwabtaka da jihar daga yammaci kudanci da kuma arewaci.

Game da aikin bada ilmi, bisa taimakon kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin a fannin inganta yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin kasashen da "ziri daya da hanya daya" ta shafa, tun daga shekarar 2015 zuwa watan Mayu na shekarar bana, yawan daliban kasashen waje da aka dauka don su yi karatu a jihar Xinjiang ya kai dubu 12 da dari 5, jihar a nata bangaren ta tura dalibai 970 zuwa kasashen waje don dalibta ko yin nazari da samun horo.

Har wa yau, a fannin kiwon lafiya, asibitoci 5 na jihar ta Xinjiang sun kaddamar da aikin samar da hidimar kiwon lafiya ga kasashen waje, wadanda suka karbi marasa lafiya na kasashen waje fiye da dubu 20. Kana asibitoci 12 na jihar Xinjiang sun shiga kawancen hadin gwiwar asibitoci na kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai.

Game da sha'anin yawon shakatawa kuma, a shekarar 2018, yawan masu yawon shakatawa da suka ziyarci jihar Xinjiang ya kai miliyan 150, wanda ya karu da kimanin kashi 40 cikin dari bisa na shekarar 2017, kuma yawan kudin da aka kashe a wannan fanni ya kai fiye da biliyan 257, wanda ya karu fiye da kashi 41 cikin dari bisa na shekarar 2017.

Rahotanni daga hukumar kwastam ta birnin Urumqi na cewa, tun daga watan Janairu zuwa watan Mayu na shekarar 2019, yawan kayayyakin da aka shiga da kuma fitar da su zuwa kasashen waje duk sun karu, musamman yawan kayayyakin da aka shigo da su cikin jihar ya karuwa sosai. Alkaluman kididdigar hukumar kwastam ta birnin Urumqi sun kuma nuna cewa, darajar kayayyakin shigi da fici a jihar daga watan Janairu zuwa Mayu na bana ta kai Yuan biliyan 52.28, wanda ya karu da kashi 10.8 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

Bayanai na nuna cewa, ana samu wannan sakamako ne, saboda yadda aka kyautata tsarin yin ciniki da kasashen waje na jihar Xinjiang, da yadda kamfanoni masu zaman kansu suka kara taka rawa a sha'anin yin cinikin waje. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China