Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron kolin dandalin raya tattalin arzikin duniya na shekarar 2019 a birnin Dalian
2019-07-04 14:44:59        cri

 

An gudanar da taron shekara-shekara na sabbin jagororin dandalin raya tattalin arzikin duniya na 2019 a birnin Dalian dake lardin Liaoning, na kwanaki uku, wanda ya gudana daga 1 zuwa 3 ga watan nan. Taken taro na wannan karo shi ne "Karfin jagoranci: Hanyar samun nasara a sabon yanayin da duniya ke dunkulewa waje guda." Yayin taron, an shirya taruruka da dama dake da nasaba da kasar Sin, ciki hadda taro mai taken " Yadda za a kafa sana'ar hada-hadar kudi ta kasar Sin a nan gaba" da taro mai taken "Mai da hankali kan hanyar kirkire-kirkire da Sin take bi" da sauransu. Mahalarta taro na ganin cewa, yanzu tattalin arzikin duniya yana dunkulewa waje guda, kuma babu wanda zai dakatar da wannan tsari, kasuwannin Sin za su ci gaba da samarwa masu zuba jari na kasashe daban-daban damammaki masu kyau na yin kirkire-kirkire.

Dandali na wannan karo shi ne karo na 13 da aka gudanar da shi a nan kasar Sin, inda aka shirya abubuwa da dama dake da alaka da kasar Sin, kuma taron ya gayyaci masana kimiyya da dama don tattauna na'urori masu sarrafa kansu, da fasahar 5G da dai sauransu. Babban direktan zartaswa na dandalin Adrian Monck ya shedawa manema labaran CRI cewa, Sin na da fasahohi da dama a wannan fanni, wadanda suka zama abin koyi ga duk duniya, ya ce:

"Sin kasa ce dake ba da babbar gudummwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, kana ta kasance babban karfi dake ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Haka kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin tana da babbar tasiri a fannin fasaha da kwadago ga duk fadin duniya. Muna fatan tattauna yadda kasar Sin take samun ci gaba zai taimakawa sauran kasashe, da ma yadda za su koyi nasarorin da Sin take samu. "

Jami'i mai kula da juyin juya halin raya masana'antu karo na hudu na dandalin Mista Murat Sonmez ya kwashe shekaru da dama yana aiki a Silicon Valley na Amurka, inda ya hada kai da wasu masana a fannin kimiya da fasaha da kamfanonin Sin, kuma ya dauki masana Sinawa da dama aiki a cibiyarsa dake nazarin kimiyya a Amurka. A ganinsa, akwai abubuwa masu kyau da za a koya daga kasar Sin ta fuskar kawar da talauci, kuma yanzu haka Sin tana kan gaba a fannonin kimiyya da fasahohi. Ya ce:

"Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannoni da dama, alal misali, a shekarun baya-bayan nan, Sin ta samu ci gaba mai armashi wajen kawar da talauci. A sa'i daya kuma, duk da sabbin kalubale da Sin take fuskantar, ciki hadda yadda Sin ta samun bunkasuwar tattalin arziki da al'umma, da bunkasuwa ba tare da gurbata muhallin halittu ba, kasar Sin na kokarin neman hanyar raya kanta bisa radin kanta. Kaso 70 cikin 100 na mahalartan taro na wannan karo suka fito daga kasashen ketare ko sauran yankuna ne, kuma sun nuna matukar sha'awa ga ci gaban da kasar Sin take samu. Sin na bukatar kara fahimtar duniya, matakin da ya samar da zarafi mai kyau wajen hada kai da sauran kasashe don samun moriya tare."

Ya zuwa yanzu, duniya na kara fuskantar wasu matsaloli ciki hadda manufar nuna ra'ayin kashin kai da ta kariyar cinikayya, matsayin da Sin take dauka na nacewa ga dunkulewar duniya na jawo hankalin kasa da kasa. Abhniav Kumar, babban jami'i mai kula da kasuwar kasa da kasa na kamfanin ba da shawara na TATA, mazaunin Belgium, wannan shi ne karon farko da ya halarci wannan taro, ya ce, a kan tattauna batun tattalin arziki da kimiyyar kasar Sin a Turai, kuma ba za a iya kawar da kasar Sin ba ko kadan a halin yauzu da duniya take kara dunkulewa waje guda. Yana kuma dora muhimmanci sosai kan bunkasuwa da yadda kasuwar kasar Sin take sauyawa, a wannan karo yana fatan ganin yadda kasuwar kasar Sin take kasancewa. Ya ce:

"Kamfaninmu ya kwashe shekaru da dama yana gudanar da hada-hada a kasuwar kasar Sin, muna kara habaka ayyukanmu a Sin saboda yadda kasuwarta take sauyawa, ina farin cikin shiga wannan aiki sosai. Duniya tana daukar kasar Sin a matsayin wani babban zarafi a gare su, saboda ganin yadda aka tsai da ajandar DAVOS, inda aka sha tattauna batutuwa dake da nasaba da kasar Sin, matakin da ya kasance wani muhimmin lokaci ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Yanzu watanni shida ke nan, ba ma kawai muna kallon tushen tattalin arzikin kasar Sin ba, har ma muna dora babban muhimmanci kan yadda kasar Sin take goyon bayan aikin dunkulewar duniya."

Alkaluman kididdiga da ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa, a farkon watanni 5 da suka gabata, yawan jarin wajen da Sin ta yi amfani da shi ya zarce dala biliyan 360, wanda ya karu da kashi 6.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu, yawan jarin wajen da sana'ar kimiyya da fasahar Sin ta yi amfani da shi ya karu da kashi 50 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Sebastian Buckup tsohon jami'i mai kula da ayyukan samun bunkasuwa da ayyukan kwadago a MDD, ya ziyarci Sin da Switzerland bayan ya kama aiki a matsayin shugaban ayyuka na dandali, lamarin da ya sa ya dora muhimmanci sosai kan yadda kasuwannin kasar Sin ke sauyawa, ya san yadda Sin take bunkasa a bana, a ganinsa, kasuwar Sin za ta samun ci gaba nan gaba, kuma za ta kasance jagora a fannin kirkire-kirkire. Ya ce:

"Babban kalubalen da bunkasuwar tattalin arzikin Sin ke fuskanta shi ne sauya hanyar samun bunkasuwa daga matakin dogaro da jari zuwa matakin dogaro da kirkire-kirkire, har ma da samar da hakikanin kayayyaki dangane da hakan. Sin ita ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, tana kuma ci gaba da bunkasuwa, tare da ba da jagoranci a wasu fannoni, ciki hadda na'urori masu sarrafa kansu, don haka ya kamata kasashen duniya su yi kokarin cin gajiya da kuma yin koyi da fasaha da kimiyyar kasar Sin". (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China