Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje kolin tattalin azriki da ciniki na farko tsakanin Sin da Afirka
2019-07-04 14:35:51        cri

A ranar Alhamis 27-29 ga watan Yulin shekarar 2019 ne, aka kaddamar da bikin baje kolin tattalin arziki da ciniki karo na farko tsakanin kasashen Sin da Afirka a birnin Changsha na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.

Bikin baje kolin, ya samar da wata dama ta inganta hadin gwiwa da musayar moriyar juna, da baje kolin miliyoyin hajoji, a wani mataki da kulla hadin gwiwar cinikayya cikin sauki tsakanin sassan biyu.

A rana ta biyu na bikin baje kolin kasashen Afrika da dama sun baje kolin kayayyakin da suke samarwa wadannan ke matukar jan hankalin kasuwannin kasar. Kayayyakin sun hada da nau'o'in kayan amfanin gona, ma'adinai, tufafin gargajiya da dai sauransu.

An kuma kulla yarjeniyoyi 84 da darajarsu ta kai Dala biliyan 2.8 a fannonin aikin gona da yawon shakatawa da sauransu. Haka kuma an shirya ayyuka 14 da suka hada da bikin bude taron, tarukan karawa juna sani, da dandaloli da baje kolin hajoji.

Masana da 'yan kasuwa da jami'ai daga kasashen Sin da Afirka sun tattauna sabbin matakan inganta alaka a tsakaninsu. Kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar raya masana'antu ta MDD, shirin samar da abinci da kungiyar cinikayya ta dunita duk sun aiko da wakilansu wajen bikin.

Baki sama da 100,000 da 'yan kasuwa, ciki har da wasu daga kasashen Afrika 53 ne suka halarta.

A sakon murnar bude bikin da ya aika, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, an kirkiro bikin baje kolin wanda aka sanar yayin taron kolin Beijing na tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) da aka yi a watan Satumban bara domin samar da dandalin zurfafa hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar tattalin arziki, cinikayya, da zuba jari don moriyar alummomin bangarorin biyu daga dukkan fannoni.

Baje kolin tattalin arziki da cinikayyar shine irinsa na farko da ya gudana tsakanin Sin da kasashen Afrika, ya kunshi jami'an gwamnatocin bangarorin biyu da masana da 'yan kasuwa da cibiyoyin hada-hadar kudi, inda aka yi musayar ra'ayoyi da tattauna muhimman hanyoyin hadin gwiwa da juna a daidai lokacin da duniya ke fuskantar fargaba game da tattalin arziki. (Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China