Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dole ne a yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka tayar da hankali a Hong Kong
2019-07-03 14:17:03        cri

A ranar 1 ga watan Yuli, an yi wani mummunan tashin hankali a yankin Hong Kong na kasar Sin, inda tsageru masu tattsauran ra'ayi suka toshe manyan tituna, da kai wa 'yan sanda hari ta hanyar amfani da gari mai guba. Kana suka kutsa kai cikin babban ginin majalisar dokokin yankin na Hong Kong, har ma suka lalata kayayyakin ginin kamar yadda suke so. Lamarin karya doka ya girgiza tare da fusanta al'umma sosai. Bayan abkuwar tashin hankalin, sassan al'umma daban daban sun yi kakkausan suka kan yadda aka yi amfani da karfin tuwo, kuma sun bukaci bangaren 'yan sanda da ya gudanar da bincike sosai kana ya yanke hukunci mai tsanani ga wadanda ake tuhumarsu da aikata lamarin.

A yayin da ake murnar ranar cika shekaru 22 da dawowar yankin Hong Kong kasar Sin a ranar 1 ga watan Yuli, wasu tsageru masu tsattsauran ra'ayi sun ta da hankali, inda suka lalata ginin majalisar dokoki bisa hujjar nuna rashin yarda da gyaran fuska kan wasu ayoyin doka, lamarin da ya nuna makarkashiyarsu. Lu Weicong, shugaban sashen kula da harkokin 'yan sanda na gwamnatin yankin musamman na Hong Kong ya bayyana cewa, ya fusata matuka da yadda aka lalata ginin majalisar dokokin. A nasa bangaren, Farfasa Chen Hongyi na kwalejin koyar da ilmin dokoki ta Jami'ar Hong Kong ya siffanta lamarin da rashin tausayi, duba da yadda masu tashin hankali suka fasa gilasan kofar ginin, suka kuma kakkarya shingen karfe, suka shafa wa alamar yankin Hong Kong kazanta, suka kuma lalata hotunan shugabannin majalisar na baya da na yanzu, kana suka rubuta kalmomin batanci a jikin bango. Dukkan mambobin majalisar gudanarwar yankin da wadanda ba jami'an gwamnati ba sun bayyana cewa, lallai lamarin ya saba doka sosai.

Wannan lamarin tashin hankali ya saba dokokin Hong Kong, ya kuma saba tsarin zamantakewar al'ummar yankin, da ma kawo illa sosai ga babbar moriyar yankin. Babu shakka wannan takala ce ga manufar "kasa daya amma tsarin mulkin biyu" kiri da muzu. Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, gwamnar yankin ta yi tsokacin cewa, dole ne a gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu. Ban da wannan kuma, 'yan majalisar dokoki 42 dake goyon bayan manufar ta yanzu sun ba da sanarwa, inda suka yi kira da kada a kawo illa ga tsarin zamantakewar al'umma. Haka zakila, kungiyoyin matasa fiye da 60 sun yi kira ga 'yan sanda da su hanzarta gudanar da bincike domin sake samar da kwanciyar hankali da tafiyar da harkoki bisa doka a Hong Kong. Gaskiya, masu tsattsauran ra'ayi sun riga sun fusata al'umma, ba za su samu goyon baya ko kadan ba.

Mazauna Hong Kong na da 'yancin yin zanga-zanga bisa doka. Dukkan zanga-zangar da aka yi a yankin a shekarar da ta gabata ta gudana cikin lumana ba tare da nuna karfin tuwo ba. Gwamnatin yankin ma tana dora muhimmanci kan ra'ayin jama'a, wadda ke da niyyar kai zuciya nesa da yin hakuri domin hada kai tare da jama'a. Amma ba za a zuba ido tana ganin wasu na tayar da hankali bisa hujjar zanga-zanga ba. Jaridar Ming Pao ta Hong Kong ta rubuta wani sharhi dake cewa, tashin hankali tashin hankali ne, bai kamata a fake da batun tashin hankali don a karya doka ba, dole ne al'umma su tashi tsaye su bambanta su, bai kamata a yi dari-dari da wannan batun ba.

Zamantakewar al'ummar Hong Kong na da al'adu daban daban, ba abin mamaki ba ne a samu mabanbantan ra'ayoyi har ma da sabani mai tsanani. Amma masu tsattsauran ra'ayi sun nuna karfin tuwo domin wai za a yiwa wasu daga cikin dokokin yankin kwaskwarima, a maimakon hakan, suna da makarkashiyar lalata manufar "kasa daya amma tsarin mulkin biyu" da yadda gwamnatin yankin ke tafiyar da harkokinta, har ma wasu kalilan sun cimma makircinsu a siyasance. Amma ba za a iya karyata da ma tsorata da mazauna Hong Kong ba, ganin yadda suke da basira da sanin ya kamata. Haka kuma ba za a iya ta da hargitsi ga wadata da zaman karko a Hong Kong ba, ya kamata a kara fahimtar muhimmancin adalci da kwanciyar hankali.

Hong Kong yanki ne da mutane kusan miliyan 7.4 ke zaune a cikinsa, kuma wani muhimmin bangare ne na kasar Sin, wanda dukkan Sinawa kusan biliyan 1.4 ke mayar da hankali a kai. An samu kyawawan sakamako kan yadda ake tafiyar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a Hong Kong a shekaru 22 da suka wuce. Ganin yadda Hong Kong ya kara samun ci gaba yayin da al'ummar Sin ke kokarin samun farfadowa, wanda buri ne na dukkan jama'a. Gwamnatin tsakiya ta Sin ta nuna goyon baya sosai ga gwamnatin yankin Hong Kong da bangaren 'yan sanda na yankin wajen daidaita lamarin tashin hankalin, domin a sake maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China