Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin zata kara bude kofa ga baki masu zuba jari
2019-07-02 15:28:15        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar za ta kara bude kofa da tabbatar da adalci da saukakawa baki masu zuba jari, sannan za ta kara inganta muhallin kasuwanci.

Li ya yi wannan bayani ne da yake bude taron shekara shekara na dandalin the New Champions 2019 ko The Summer Davos Forum, wanda ke tattauna batutuwan tattalin arzikin duiniya, da ya gudana a birnin Dalian na kasar Sin.

Firaministan ya ce kasar Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen fadada bude kofa ta kowanne bangare.

Ya ce kasar za ta mara baya ga zuba jarin waje a bangarorin da suka hada da fasahar adana bayanai ta zamani da kera kayayyakin aiki da hada magunguna da samar da sabbin kayayyaki da kuma yankunan tsakiya da yammacin kasar, yana mai cewa, za a gabatar da manufofi masu sauki da suka shafi bangaren sayen kayayyakin aiki daga ketare domin amfanin kashin kai da harajin kamfanoni da kuma samar da filaye. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China