Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin ya gina unguwar zamani a Angola domin kyautata rayuwar al'ummun kasar
2019-07-02 11:03:13        cri

Yanzu haka kamfanin gine-gine na CITIC na kasar Sin yana gudanar da wani babban aikin gina unguwar zamani a kudancin Luanda, babban birnin kasar Angola, inda ake gina gidajen kwana da makaranta da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, a wani mataki na inganta rayuwar mazauna birnin.

A unguwar dake kudancin birnin Luanda na Angola, an ga wasu sabbin gine-ginen da ake ginawa, kamfanin gine-gine na CITIC na kasar Sin ne yake gudanar da wannan babban aikin, wanda ake kira sabon garin Kilamba, garin dake da fadin mubara'in mita miliyan 3 da dubu 310, gaba daya an gina gidajen kwana da yawansu ya kai 710, inda za a samar da gidajen kwana sama da dubu 20 da kantuna fiye da 200, kana domin biyan bukatun mazauna wurin, an kuma gina wata makaranta da wasu manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, kamar su tituna, da kamfanin samar da ruwa, da kamfanin tsabtace ruwa, da kamfanin samar da wutar lantarki da sauransu.

Mataimakin babban manajan sashen kula da aiki na kamfanin CITIC reshen Afirka Guo Sen ya yi mana bayani cewa, sabon garin Kilamba shi ne aikin gini na farko da kamfaninsa ke gudanarwa a Angola, aikin da zai amfanawa al'ummun kasar da yawansu ya kai dubu 120, yana mai cewa, "Hakika kamfaninmu ba aikin gine-ginen kawai yake yi ba, yana la'akari da tsarin birnin, alal misali samar da ayyukan yi da gina tituna da samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da sauransu, a takaice dai ana iya cewa, muna gudanar da aikin ne bisa manyan tsare-tsare."

An fara gudanar da aikin ne tun daga shekarar 2008, a wancan lokaci,ba dade da kammala yakin basasa a kasar ta Angola ba, a don haka kasar tana fama da matsalar karancin kayayyaki, musamman ma kayayyakin gine-gine, domin ganin aikin ya gudana, kamfanin CITIC na kasar Sin ya yi kokari matuka inda ya yi jigilar kayayyakin da ake bukata daga kasar Sin, a sa'i daya kuma, kamfanin ya zuba jari domin kafa kamfanonin samar da kayayyakin gine-gine a Angola, ta yadda zai gudanar da aikin cikin lumana, Guo Sen ya kara da cewa, "Muna aikin gine-ginen ne bisa ma'aunin kasar Sin, kuma alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, gaba daya nauyin kayayyaki kamar karafa da simenti da aka yi jigilar su zuwa wurin daga kasar Sin ya kai sama da tan miliyan 4, ban da haka mun kafa wasu kamfanonin samar da barbashin duwatsu a wurin domin samar da kayayyakin gine-ginen da muke bukata."

An kammala aikin gina gidajen kwana a sabon garin Kilamba a shekarar 2012, kana domin kyautata aikin tafiyar da harkokin garin na gwamnatin Angola, kamfanin CITIC shi ma ya kafa wata cibiyar samar da hidima ga mazauna garin, inda ake samar da hidimar gyara gidajen kwana, Guo Sen yana ganin cewa, kokarin da kamfaninsa ke yi ya nuna cewa, yana sauke nauyin dake bisa wuyansa wajen kyautata rayuwar al'ummun kasar ta Angola, a cewarsa: "Yayin da kamfanin CITIC ke gudanar da aikinsa a Angola, ya taba hayar ma'aikatan da yawansu ya kai dubu 17 a wurin, lamarin da ya samar da guraben aikin yi da yawan gaske, kana domin kyautata kwarewarsu, mun horas da su a bangaren fasaha, har wasu daga cikinsu sun kasance ma'aikatan fasaha, yanzu haka wasu sun riga sun tafi wasu kamfanonin kasar Sin ko kamfanonin Spaniya da Brazil domin ci gaba da aiki da su."

Hakazalika, a shekarar 2014, kamfanin CITIC ya kafa wata makarantar horas da sana'a a kasar, inda ake samar da hidima kyauta ga daliban dake fama da talauci, kawo yanzu daliban da suka kammala karatu a makarantar sun kai sama da 400.

Isidro Angostinho, mai shekaru 21 da haihuwa, yana koyon ilmin sana'ar lantarki ne a makarantar, ya gaya mana cewa, ya samu damar karatu kyauta a makarantar ne bisa tallafin kamfanin kasar Sin, bayan ya kammala karatun, zai nemi aiki domin ba da gudumowarsa ga ci gaban rayuwar al'ummar kasarsa, yana mai cewa, "Ina fatan zan samu damar yin aiki a kamfani kamar kamfanin CITIC na kasar Sin, idan na samu isasshen kudi, zan kafa wani kamfani domin samar da karin guraben aikin yi ga sauran mutane, ta yadda za mu ciyar da kasar Angola gaba."

Tsohon shugaban Angola Dos Santos ya taba bayyana cewa, unguwar zamanin da kamfanin kasar Sin ya gina ta kasance wata lu'u-lu'un kasar, da ma fadin Afirka baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China