Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Syria ta mayar da martani kan harin makamai masu linzami na Isra'ila
2019-07-01 10:55:38        cri

Makaman kare hari ta sama na Syria, sun mayar da martani kan sabon harin makamai masu linzami da Isra'ila ta kai kan sansanonin soji dake kusa da birnin Damascus da kuma yankin tsakiyar lardin Homs.

Makaman sun dakile harin da aka yi niyyar kai wa yankin kudu maso yammacin birnin Damascus, inda suka yi nasarar kakkabo makamai masu linzami 6.

Har ila yau, makaman na Syria, sun dakile yunkurin wani harin da aka kai tsakiyar lardin Homs a lokaci guda.

Gidan talabijin na Syria ya ruwaito cewa, jiragen yakin Isra'ila ne suka kai hare-haren daga cikin sararin samaniyar kasar Syria.

Rahoton ya ce, wasu daga cikin kayayyakin fararen hula kamar gidaje, wadanda ke wajen birnin Damascus, sun lalace.

Ba wannan ne harin makami mai linzami na farko da aka kai Syria ba, la'akari da hare-haren makamai masu linzami da Isra'ila ke kai wa kan sansanonin sojin Syria. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China