Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sa Kaimi Ga Shawarwarin Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakanin Sin Da Amurka Bisa Tushen Girmama Juna
2019-06-29 20:28:27        cri

A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron koli na kungiyar G20 a birnin Osaka a yau Asabar, ya gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, inda suka amince da sake yin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu bisa tushen adalci da girmama juna. Kasar Amurka ta bayyana cewa, ba za ta kara buga sabon harajin kwastam ga kayayyakin da Sin ke shigarwa kasar ba. Tawagogin wakilan kasashen biyu a wannan fanni za su tattauna kan batun a nan gaba.

Sake yin shawarwarin tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Amurka ya shaida alama mai kyau, wadda ta dace da ra'ayoyin jama'ar kasashen biyu da fatan kasashen duniya, domin hakan zai sassauta matsin lambar da ake fuskanta a kasuwa.

A matsayin kasashe biyu mafi karfin ci gaban tattalin arziki da cinikayya a duniya, ba abin mamaki ba ne idan Sin da Amurka sun fuskanci matsaloli yayin da suke hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya. Ya kamata kasashen biyu su yi shawarwari cikin adalci, da girmama juna, da daidaita matsalolinsu, da kuma sa kaimi ga hadin gwiwarsu. A cikin shekara fiye da daya da suka gabata, Sin ta nuna sahihanci ga batutuwan da ke jan hankalin kasar Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, tare da kokarin cimma yarjejeniyar da bangarorin biyu suke iya amince da ita. Amma sai kasar Amurka ta kara matsa mata lamba, lamarin da ya kawo illa ga shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, kana ya kawo hadari ga duniya ta fuskar koma bayan tattalin arziki.

Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, kara saka haraji ba zai iya warware matsala ba, sai dai a tsananta matsalar kawai. Tattaunawa cikin daidaito hanya ce daya tak ta warware matsalar cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Sake maido da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka na shaida cewa, za a koma hanyar da ta dace wajen warware matsalar. Amma, takaddamar cinikayya tsakanin Sin da Amurka na da sarkakiya, dole ne a yi kokari ba tare da kasala ba, domin warware ta baki daya.

Sin na nuna sahihanci wajen ci gaba da yin shawarwari da Amurka, amma ya kamata shawarwarin ya kasance bisa daidaito, da girmama juna, da ma warware batutuwan da bangarorin biyu ke mayar da hankali da damuwa a kai. Wato ya kamata bangarorin biyu su kasance a matsayi na daidai wa daida, sannan sakamakon shawarwarin ya amfanawa bangarorin biyu. Bai kamata wani bangare ya matsawa daya lamba, kana kada sakamakon shawararin ya amfanawa bangare daya kadai. A waje daya kuma, ya kamata bangarorin biyu su lura da abubuwan da junansu ke dora muhimmanci a kai, wato kada a saba wa manufar juna. A cikin wata guda da ya gabata ma, kasar Sin ta dauki jerin matakai don tinkarar tsanantar takaddamar cinikayyar, lamarin da ya nuna cewa, a kan batun da ya shafi cikakken 'yanci da mutuncin kasar, dole ne kasar ta kare babbar moriyarta ba tare da tsoron komai ba.

A wurin ganawar shugabannin kasashen Sin da Amurka, Trump ya bayyana cewa, Amurka ba za ta kara sanya haraji kan kayayyakin da Sin za ta shigar kasar ba, lamarin da ya sake farfado da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu. Nan gaba kuma, abu mafi muhimmanci shi ne Amurka ta cika alkawarin da ta dauka, ta sanya kokari tare da kasar Sin, ta yadda kasashen biyu za su samu sakamako mai gamsarwa. Tun bayan da kasashen biyu suka daddale huldar diplomasiyya dake tsakaninsu shekaru 40 da suka gabata, an kara fahimtar cewa, idan sassan biyu suka hada kai, to za su samu moriya tare, amma idan suka yi adawa da juna, to ba shakka za su yi hasara tare. A bayyane yake cewa, hadin gwiwa ya fi takaddama, ko kuma tattaunawa ta fi adawa, kasashen nan suna iya daidaita sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa kadai, saboda hakan zai amfanawa kasar Sin, haka kuma zai amfanawa kasar ta Amurka, har ma zai amfanawa dukkan duniya baki daya. Ana fatan tawagogin wakilan tattaunawar sassan biyu za su kara mai da hankali kan damar farfado da tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, domin tabbatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a wurin ganawar, ta hanyar daukar hakikanan matakai, bisa tushen martaba juna, da haka za su kara karfafa fahimtar juna, tare kuma da ciyar da tattaunawar gaba cikin lumana.

A wurin taron kolin shugabannin kasashen mambobin kungiyar G20 na Osaka, shugaba Xi Jinping ya sanar da matakai guda biyar da kasar Sin za ta dauka domin kara bude kofarta ga kasashen waje, hakika wannan shiri ne da kasar Sin ta tsara kafin taron, yanzu dai ko za a samu sakamakon tattaunawar, ko ba za a samu ba, har kullum kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin raya kasa da ta tsara, ta hanyar yin gyaran fuska, tare kuma da dakile daukacin kalubale da rikicin da take fuskanta. (Zainab, kande, Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China